An damke wanda ya yi ‘kashin’ kullin hodar Ibilis 59 a filin jirgin saman Abuja

0

Hukumar Hana Sha da Fataucin Muggan Kwayoyi (NDLEA) ta kama wani matashi mai suna Okoguale Douglas da ya rika sako kashin kulli hodar ibilis har kulli 59 a filin jirgin saman Abuja.

A gwajin nauyin hodar ibilis din da douglas mai shekaru 23 da yi kashin su sun kai giram 781.2.

Jami’in yada labarai na hukumar Femi Babafemi ya sanar da haka a wani takarda da ya raba wa manema labarai ranar Juma’a.

Ya ce NDLEA ta kama wannan matashi yayin da yake kokarin shiga jirgi kasar Italy daga Najeriya.

“Binciken da NDLEA ta gudanar akai ya nuna cewa Douglas ya hadiye kullin hodar ibilis inda dole suka tilasta shi ya yi bahayansu.

Babafemi ya ce sakamakon bincike ya nuna cewa Douglas ya fara zama a kasar Italy a shekaran 2011 tare da ‘yan uwan mahaifinsa.

Ya ce Douglas ya dawo Najeriya ranar 4 ga Afrilu domin yin jana’izan mahaifin da ya rasu kwanannan.

“Douglas ya ce ya karbi hodar ibilis din ne a Abuja wajen wasu mutane da Bai taba ganin su ba, zai kai musu kasar Italiya.

Babafemi ya ce hukumar za ta ci gaba da yin bincike domin gano sauran mutanen dake da hannu akai.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda NDLEA ta kama hodar ibilis mai nauyin giram 140 da aka boye a gunkin ‘Mary’ wanda ake inkari da ita ce mahaifiyar Yesu.

Darikan Katolika na amfani da gunkin Mary mahaifiyar Yesu wajen yin adu’o’i domin a wurin su Mary ita ce ta haifo mai ceton su.

Sai dai wannan karon wasu kangararrun mutane sun dirka wa gumakan Mary din kwayoyi domin yin safarar su zuwa kasashen waje.

Hukumar NDLEA ta kama gunkin a tashar jiragen saman Abuja a hanyar waske wa da su kasar Philippines.

Share.

game da Author