Gwamnan jihar Kaduna ya lashi takobin cewa lallai ba zai hakura da zanga-zangar da kungiyar kwadago ta yi a jihar ba sai ya maka ta kotu sannan kuma maganan zaftare ma’aikata nan daram dam.
Gwamna El-Rufai ya bayyana haka a jawabin da ya yi ranar Juma’a a Kaduna.
Idan ba a manta, PREMIUM TIMES HAUSA ta kawo muku labarin yadda kungiyar kwadago ta gudanar da zanga-zanga a jihar Kaduna wanda yayi sanadiyyar dakatar da muhimman ababen more rayuwa a jihar Kaduna da suka hada dakatar da raba wutyar lantarki, rufe makarantun jihar da asibitoci da dai sauransu.
” Ina mai godiya gareku mutanen jihar Kaduna saboda irin goyon bayan da kuka ba gwamnati a lokacin da kungiyar kwadago ta mamaye jihar mu. Ta saka mutane cikin matsin da ba su shirya wa ba.
” Muna godewa shugabannin jihar da masu fada aji hadi da sarakunan mu da suka yi tsayin daka wajen tausa mutane a lokacin yajin aikin.
” Mu na taya ‘yan jihar jimamin matsalolin da aka fada a sanadiyyar rashin wutar lantarki da ya kawo wa mutanen jihar cikas a al’amurorin su na yau da kulluma wanda ba ahaka a ka shirya wa ba.
” Jihar Kaduna ta yi wa ma’aikatan jihar gatan da wasu jihohin ba su yi wa ma’aikatan su irin haka ba. Mune muka fara biyan naira 30,000 a matsayin mafi kankantar albashi a fadin kasar nan, harda kananan hukumomin jihar 23 sannan kuma muka kara kudin fanshon wadanda suka yi ritaya zuwa naira 30,000.
” Jihohi da yawa basu iya biyan naira 30,000 a matsayin mafi kankantar albashi ba, wasu da suka fara biya sun dakatar amma mu muna biya. Kungiyar Kwadago bata je wadancan jihohi ta yi zanga-zanga ba sai jihar Kaduna saboda kawai su hargitsa man jiha da son zuciya.
” Abinda muke so kowa ya sani shine jihar Kaduna ba za ta ci gaba da kashe akalla kashi 84 zuwa kashi 96% na kudaden da ta ke karba daga Abuja kan wasu mutane sa basu wuce kashi 1% na yan Kaduna ba, sauran kuma ko oho.
” Saboda haka za mu rage yawan ma’aikata a jihar, wannan babu ko tantama akai, yanzu haka ana duba takardun duka ma’aikatan jihar ana tankade da rairaya, ana cire takardun wadanda suka shiga aiki da jabun takardu, da wadanda takardun su bai cika da masu karbar albashi na babu gaira babu dalili kuma basu yin aikin komai ba.
” Bayan su zamu zaftare ‘yan siyasa da aka nada suma.