Shugaban kwamitin dattawan jam’iyyar PDP, kuma sarkin Fulanin Nasarawa, Walid Jibrin ya bayyana cewa yawon kiwo da fulani makiyaya ke yi a yanzu ya zama tsohon yayi.
Walid ya ce an ci gaba yanzu a duniya, yawon kiwo ya zama tsohon yayi, shima matsayar sa daidai yake da na gwamnonin yankin kudancin Najeriya da suka hana yawon kiwo a jihohin su.
” A matsayi na na shugaba kuma mai fada aji a kungiyar Makiyaya na Fulani, kuma a matsayina na bafulatanin asali, ina so in sanar cewa a wannan lokaci da muke ciki yawon kiwo ba zai yi tasiri ba kamar da. Ya zama tsohon yayi dole a samar da mafita.
Ya kara da cewa abinda ya sa yawon kiwo bai zama abin damuwa ba a da shine don a da makiyaya basu da yawa haka kuma manona. Amma yanzu an yi yawan da yawon kiwo ba zai hyiwu ba.
” Dole ne fulani makiyaya su yi karatun ta natsu, su kirkiro hanyoyin da za su musanya yawon kiwo da su domin wannan tsari ya zama tsohon yayi.
” Maimakon a rika sukan ‘yan kudu da suka hana yawon kiwo a jihohin su, gode musu ya kamata a yi kuma a yaba musu saboda kyakyawan manufa da suke da shi maimakon a rika sukan su ana yi musu kaman batanci don sun hana kiwo.