Buhari, Malami, El-Rufai sun yi alhinin rasuwar Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Attahiru

0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari tare da Ministan Shari’a Abubakar Malami sun yi alhinin rasuwar Babban hafasan Sojojin Najeriya Janar Ibrahim Attahiru.

Attahiru ya rasu a Kaduna a sanadiyyar hadari jirgin sama da yake ciki tare da wasu manyan sojoji jim kadan bayan tashi.

Buhari ya ce rasuwar Attahiru babban rashi ne ga Kasa Najeriya. Ya yi fatan Allah ya jikan sa Amin.

Haka shima, gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya mika ta’aziyyar sa ga Iyalan marigayin.

” Wannan babban rashi ga Kasa. Ina rokon Allah ya ji kansa, ya sa Aljanna ta zamo makoma.

Haka nan shima Abubakar Malami ya bayyana irin yadda sanarwar rasuwar Attahiru ya girgiza shi.

Ya yi adduar Allah ya ji kan mamacin.

A sanrwar da rundunar Soji ta fitar ranar Juma’a, Attahiru ya rasu ne tare da wasu manyan sojoji 10.

” Rundunar Sojin za ta ba da cikakken bayani a kai nan ba da dadewa ba.” In ji Yerima, Kakakin rundunar.

Share.

game da Author