KOWA DA ABIN DA YA DAME SHI: APC ta kafa kwamitin mutum 61 domin cin zaben 2023

0

Yayin da rikice-rikice da kashe-kashe su ka yi kamari a kasar nan cikin halin rashin tsaro, tare da zaman dar-dar na yawan garkuwa da mutane a karkashin mulkin APC, a gefe daya kuwa jam’iyyar mai mulki ta kafa kwakkwaran kwamiti mai kunshe da mutum 61.

Wannan kwamiti dai ba matsalar da kasar nan zai zauna nemo mafita ba, zai yi aikin sake saisaita jam’iyyar APC ne ya karfafa ta, yadda samun nasara a zaben shugaban kasa na 2023 ba zai yi wa jam’iyyar wahala ba.

Aikin wannan kwamiti shi ne tuntubar juna da masu ruwa datsakin jam’iyya da kuma tsare-tsaren kitimirmirar yadda za a ci zaben 2023.

Wata sanarwa Babban Sakataren APC, John Akpanudoehede ya fitar a ranar Litinin a Abuja, ta na dauke da sunayen wadanda aka nada ckin wannan kakkarfan kwamitin.

Sakataren ya kara da cewa Shugaban Riko na Jam’iyyar APC, kuma Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala-Bun ne zai rantsar da mambobin kwamitin a ranar Talata, a babbar sakateriyar APC da ke Abuja.

Yayin da Gwamna Mohammed Badaru na Jigawa zai kasance shugaban kwamiti, Ikechi Emenike zai zama sakataren kwamiti.

Wasu daga cikin ’yan kwamitnin sun hada da gwamnonn da su ka kunshi Yahaya Bello na Kogi, Babagana Zulum na Borno, Inuwa Yahaya na Gombe, Aminu Masari na Katsina, Simon Lalong na Plateau, Hope Uzodinma na Imo, Babajide Sanwo-Olu na Lagos, David Umahi na Ebonyi da Abdullahi Ganduje na Kano.

Akwai kuma Matamakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ovie Omo-Agege, tsoffin Kakakin Majalisar Tarayya biyu, Dimeji Bankole da Yakubu Dogara duk za su kasance cikin kwamitin su ma.

Yanzu dais aura shekaru biyu cur a yi wannan zabe, wanda jam’iyya mai mulki, APC ta fara shirin sake yin nasara a kan sa tun yanzu.

Share.

game da Author