BANDA TURERENIYA KOWA ZAI SAMU: Kamfanin MTN ya tallafa wa Najeriya da allurar AstraZeneca miliyan 1.4

0

Kamfanin MTN ya taimaka wa kasashen Afrika da allurar rigakafin korona har milyan 7, wadanda daga cikin su ne aka bai wa Najeriya kwalabe 300,000 domin a ci gaba da dirka wa jama’a rigakafin cutar korona.

Shugaban Kwamitin Shugaban Kasa mai Dakile Cutar Korona, kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ne ya bayyana haka alokacin da ya ke jawabi ga manema labarai a ranar Litinin a Abuja.

“Jiya ranar Lahadi, 21 Ga Maris, 2021, kwamitin mu na PTF ya karbi kwalaben allurar rigakafin korona na Oxford-AstraZeneca guda 300,000 daga MTN Nigeria.”

“Mun karba kuma mun nuna matukar godiya sosai, sannan kuma mu na kira ga sauran manyan kamfanoni su ma su bayar da ta su gudummawar rigakafin domin mu ci gaba da yakar cutar korona.

Wani jami’in MTN ya bayyana cewa kamfaninya raba gudummawar kwalabe milyan 7 na rigakafin korona ga kasashen Afrika, kuma ana sa ran za a bayar da har guda milyan 1.4 nan da karshen watan Maris, 2021 ga Najeriya.

A farkon watan Maris ne dai Najeriya ta karbi har guda milyan 4, kuma zuwa yanzu an fara yi wa mutum 122,000 a fadin kasar nan, yayin da ake ci gaba da raba allurar a jihohi da wasu kananan hukumomi.

Yayin da ake ci gaba da raba allurar a Najeriya, a gefe daya kuma wasu kasashen Turai na ci gaba da dakatar da zabga wa jama’a rigakafin.

A ranar Litinin kuma sai Ministan Lafiya na Najeriya, Osagie Ehanire ya bayyana cewa kamfanin AstraZeneca ya kara tabbatar wa Najeriya cewa allurar ba ta da wani aibi.

Tuni dai ake ci gaba da yin allurar a Najeriya, sai dai kuma mahukunta sun bayyana cewa ba za a litasta wa mutane cewa tilas sai mutum ya je an dirka masa allurar ba.

Sai dai kuma kasar Saudiyya ta yi sanarwar cewa duk wanda ba a yi wa rigakafin korona a kasar sa ba, to ba za a bari ya shiga kasar domin yin aikin Hajji ba.

Share.

game da Author