Najeriya ta kara kinkimo bashin dala biliyan 1 domin lamuni ga masu kanana da matsakaitan sana’o’i

0

Karin maganar da Bahaushe ke cewa ‘danyen nama baya kashe kura’, sai kara tabbata ta ke yi a Najeriya, yayin da Ministan Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Adeniyi Adebayo ya bayyana cewa Najeriya ta samo bashin dala biliyan 1 domin bayar da lamuni ga kananan sana’o’i a fadin kasar nan.

Ya ce an karbo bashin ne a karkashin kulawar Bankin Raya Masana’antu (BoI) a karkashin Ma’aikatar Masana’antu, Cinkayya da Zuba Jari.

Kakakin Yada Labarai na ministan, Ifedayo Sayo ya bayyana haka, inda y ace wannan lamuni zai bunkasa kananan masana’antu da kasuwanci (MSMEs) a bangarori daban-daban na harkokin tattalin arziki a kasar nan.

Adebayo ya bayyana cewa za a raba wannan lamuni tare da hadin guiwar wasu masu hannu daga kasashen waje, kuma bashin zai dauki tsawon lokaci kafin a gama biya.

Ya ce shirin na daga cikin kokarin da gwamantin tarayya ke yi wajen farfado da karfin tattalin arzikin Najeriya.

“A halin yanzu ana kan tattaunawa da Dunn da Bradstreet domin samar da daidaiton yadda za a bai wa masu kananan masana’antu da kasuwanci wannan lamuni.” Inji shi.

Ya kuma yi karin bayani dangane da kokarin gwamnatin tarayya wajen tallafa wa masu kananan masana’antu sakamakon jigatar da harkokin su su ka fuskanta dalilin barkewar cutar korona a kasa da duniya baki daya.

“Akwai wadanda za su ci moriyar naira 50,000, wasu 30,000 har mutum 333,000.

Wannan shiri a cewar sa zai samar da dimbin sana’o’in hannu kuma ya ceto wasu masu sana’o’in hannu kimanin miliyan 1.3 daga durkushewa.

Share.

game da Author