Kotun Koli ta kori rokon da iyalan Abacha su ka yi na a mallaka masu kudaden da su ka kimshe a kasashen waje

0

Kotun Koli ta kori karar rokon da iyalan marigayi tsohon shugaban kasa, Janar Sani Abacha su ka yi, domin a ba su damar mallakar tulin makudan kudaden da Abacha da kuma su din su suka boye a bankin Swiss da kuma wasu bankunan kasashen waje.

PREMIUM TIMES ta ruwaito cewa wani mai suna Ali Abacha ne aka shigar da karar a madadin sa, wacce Masu Shari’a biyar na Kotun Koli, a karkashin jagorancin Sylvester Ngwuta, su ka yi watsi da karar.

Babbar Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun ce ta jagoranci yanke hukuncin, inda ta ce bukatar da Ali Abacha ya gabatar ba ta wani bambanci da irin wadda Abba Mohammed Sani ya shigar, kuma Korun Koli ta yi watsi da karar a ranar 7 Ga Fabrairu, 2020.

Shi dai Abba Mohammed Abacha ya shigar da kara ce tun cikin 2010, inda ya maka shugaban Najeriya kotu, tare da Antoni Janar kuma Ministan Shari’a na lokacin a wata kara mai lamba SC/20210.

Mai Shari’a Kekere Okun ya ce an yanke hukunci, kuma ba’asin karar da Ali ya shigar bas hi da bambanci da irin na Abba.

Ta ce yadda hukunci ya yi watsi da kara ya wajaba a kan wadda Abba Mohammed Abacha ya shigar, to haka ita ma karar da Ali Abacha ya shigar ba ta da wata madogarar da za a iya tsayawa da kafafun ta.

Sani Abacha ya mutu ranar 8 Ga Yuni, 1990, kuma ya saci makudan kudaden da ya kimshe kasashen waje, don shi da iyalan sa.

Sai dai kuma bayan mutuwar ani Abacha, Najeriya ta ci gaba da karbo wadannan kudare, daga wancan lokaci har zuwa cikin Fabrairu, 2020.

A ranar 23 Ga Disamba, 1999 sai shugaban lokacin, Olusegun Obasanjo ya umarci Minsitan Shari’a na lokacin, Kanu Igabi ya kwace asusun Bankunan da aka kimshe kudaden a kashen waje.

Share.

game da Author