KWANTON BAUNA: Yadda mahara suka kashe sojoji 7 a jihar Nasarawa

0

Mahara sun kashe sojoji 7 a dajin Mararaba-Ude dake karamar hukumar Nasarawa a jihar Nasarawa.

Sojojin dake aiki a karkashin bataliya na 177 a barikin sojoji na Shitu Alao a Keffi jihar Nasarawa sun gamu da ajalinsu ne a hanyarsu ta zuwa ceto wasu mutane da mahara suka yi garkuwa da su suka arce dasu cikin dajin.

Sojoji 13 da shugaban su kaftin Felix Kura suka afka dajin domin ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.

Ashe maharan sun shirya musu kwanton bauna da dana tarko a cikin dajin inda a haka suka yi nasarar kashe mutum 7 daga cikinsu.

Cikin wadanda aka kashe akwai kaftin Kura, Sagen Saka Yakubu Bati, Kofur Kefas Iliya sannan da wasu sojoji hudu da bam da ba aiya gane su da kyau ba.

Da sojojin suka tabbatar maharan sun fi karfin su sai dayan su Kura ya umurci su su gudu.

Shugabanin bataliya ta 177 sun sanar da iyalen sojoji bakwai da aka kashe a dajin a yanzu haka.

A ranar Alhamis PREMIUM TIMES ta nemi ji daga kakakin rundunar sojin Najeriya Sagir Musa game da wannan kisa, amma ya ce har yanzu bai samu rahoto to bayanin abinda ya faru ba.

Iyalan wadanda aka kashe sun nuna jamimin rashin mazajen su da ‘yan uwan su.

Hanyar Keffi-Abuja ya baci matuka saboda hare-haren masu garkuwa da mutane.

Ranar Litini mahara sun yi garkuwa da shugaban jami’ar Anchor Johnson Fatokun.

Maharan sun yi awon gaba da Fatokun a hanyarsa ta zuwa garin Jos daga Keffi.

Mataimakin Rajistaran Jami’ar Sanusi Okesola ya bayyana cewa maharan sun bukaci a biya Naira miliyan 20 kafin su saki Fatokun.

Okesola ya ce an biya kudin diyan sai dai bai fadi ko nawa ne aka biya ba.

Share.

game da Author