GARKUWA DA MUTANE: Zulum ya ce sojoji sun kasa tsare matafiya

0

“Matukar za a ce sojoji sun kasa tsare rayukan matafiyan da tsakanin su da shiga Maiduguri bai fi kilomita 20 ba, to ni dai ban ga yadda za a yi a yadda sojojin su ke a yanzu za su iya kawo karshen ta’addancin nan da wuri ba”

Gwamna Babagana Zulum na Jihar Barno ya zargi sojoji da kasa kare gungun matafiyan da Boko Haram su ka yi garkuwa da su kusa da shiga Maiduguri cikin makon da ya gabata.

Zulum ya ce masu ta’adda na ci gaba da kashe mutane saboda sojoji sun kasa kare rayukan su.

Zulum ya na magana ne sanadiyyar sace matafiya 35 da aka yi tsakanin Damaturu da Maiduguri, daidai Jakana, kilomita 20 kafin a shiga Maiduguri.

A ranar Litinin ce Gwamna Zulum ya kai ziyara wurin da aka tare matafiyan aka yi awon gaba da 35, sannan aka kone motoci da dama.

A wurin ne gwamnan ya yi magana da manema labarai, inda ya nuna damuwar sa ganin yadda duk da dandazon sojoji da ‘yan sandan da ke kan hanyar, amma Boko Haram ba su dai kisa da sace matafiya ba.

“Abin bakin ciki ne yadda ake ci gaba da sace matafiya da karkashe su a kan titin Maiduguri zuwa Damaturu. Sannan abin takaici ne yadda ake yin wannan ta’addanci a tsakanin Jakana zuwa Auno, cikin tazarar kilomiya 20 kacal.

“Abin mamaki ga mu da Birgade Kwamanda da zaratan sa a Jakana, sannan ga mu da Kwamanda da bataliyar sa sukutum a Auno, tazatar kilomita 20 tsakani, amma a ce sojojin nan sun kasa kare lafiya da rayuka da dukiyoyin matafiya.

“Da safiyar nan tsakanin Maiduri zuwa Jakana ban ga soja ko guda daya tal ba. Hatta ‘yan sandan RRS, wadanda mu ne mu ka ba su kayan aiki da motoci domin yin sintiri, su ma babu ko daya a kan titin. Maimakon su zo su kare lafiya da dukiyoyin mutane, amma sojoji da ‘yan sandan nan ba su komai sai karbar kudade a hannun atafiya.”

“Wannan abin kunya da me ya yi kama? Ku dubi yawan motocin da aka kona fa. Abin haushi babu mai iya fitowa ya yi magana. Ka na yin magana shikenan ka zama nama.

“Matukar za a ce sojoji sun kasa tsare rayukan matafiyan da tsakanin su da shiga Maiduguri bai fi kilomita 20 ba, to ni dai ban ga yadda za a yi a yadda sojojin su ke a yanzu za su iya kawo karshen ta’addancin nan da wuri ba”

Daga Damaturu zuwa Maiduguri kilomita 135 ne. Amma zirin da za a kira lahira-kusa bai fi tazarar kilomita 20 ba.

PREMIUM TIMES HAUSA ta bada labarin yadda aka rika tare hanyar ana jidar matafiya ana nausawa daji da su fiye da sau 50 a cikin 2020.

Share.

game da Author