Gwamnati ta kara wa’adin hada layin waya da lambar katin dan kasa

0

Gwamnatin Najeriya ta sanar da karin wa’adin lokacin da za a rufe hada layin waya da katin dan kasa.

Sanarwar wanda Hukumar Sadarwa ta Kasa ta fitar ranar Litinin, ta ce an kara makonni uku daga ranar 31 ga Disamba da wadin farko zai cika zuwa 19 ga Janairu ga dukkan wanda yake da katin amma bai hada shi da layin wayar sa ba.

Sannan kuma wadanda ba su katin shaidar zama dan kasa kuma, an kara makonni shida daga 31 ga Disamba zuwa 9 ga Faburairu domin su yi katin zama dan kasa sannan su hada shi da layin su.

A karshe sanarwar ta ce, shugaba Muhammadu Buhari ya yaba wa aikin hada layin waya da katin zama dan kasa da ma’aikatar Sadarwa ta bijiro da shi a wannan lokaci.

Minista Ali Pantami da shugaban hukumar NCC Umaru Dambatta, da kuma shugabannin Kamfanonin sadarwa na Kasa duka sun halarci wannan taro.

Idan ba a manta, an ruwaito yadda masu kokarin yin rajista katin zama dan kasa suka yi tururuwa zuwa ofishin hukumar NIMC, dake Legas wanda yawan su ya sa dole aka tsaida yin rajistan.

A yayin da wasu da dama ke kokarin hada layin wayan su da katin zama dan kasa wasu basu da shi har yanzu.

Ma’aikatar Sadarwa ta Kasa ta ce duk wanda bai hada layin sa da katin shaidar zama dan kasa ba, za a dode layin sa ba zai sake aiki ba, idan har bai yi ba zuwa lokacin da aka kammala yin rajistan

Share.

game da Author