Hukumar Hisbah ta ta kama karuwai da ‘yan kwaya 43 a Kano

0

Hukumar Hisbah a Jihar Kano ta kama wasu bata gari 43 da aka samu suna aikata laifuka dabam-dabam a jihar.

Ma’aikata sun damke wadannan masu laifuka ne a Kasuwar Kwanar Gafan, dake karamar hukumar Garun Malam, dame jihar.

Kwamandan ‘yan rundunar Hisbah Harun Ibn-Syna ya bayyana cewa 34 daga cikin wadanda aka kama, mata ne sauran maza.

Ya kara da cewa a cikin su akwai mutum 14 da kae dayuke da cutar Kanjamau, wato HIV, 10 sun sani 4 daga ciki ba su ma sani ba, suna buga harkar su ne kawai yadda suka ga dama.

An kama wasu cikin su da kwalayen kwaroro roba, da kwalaben giya.

A karshe Darektan hukumar, Aliyu Kibiya ya ce ba duka wadanda aka kama ba ne ‘yan asalin jihar Kano, akwai yan asalin jihohin Adamawa, Anambra, Koross Ribas, Bauchi, Benuwai, Kaduna, Neja, Gombe da Taraba.

Share.

game da Author