Majalisar Tarayya ta sha alwashin amincewa da Kudirin Dokar Man Fetur (PIB), kafin karshen Maris 2021

0

Majalisar Tarayya ta tabbatar da cewa kafin karshen watan Maris, 2021 za ta amince tare da mika Kudirin Dokar Fetur (PIB).

Shugaban Kwamitin kuma Bulalar Majalisar Tarayya, Tahir Monguno ne ya bayyana haka wurin zaman kwamitin.

A ranar Talata ne Majalisar Tarayya ta mika kudirin bayan an yi masa karatun tilawa maimaici na biyu, sannan ta ce kwamiti ya je ya sake dubawa, kafin a sake maida shi majalisa a yi masa tilawar karshe.

A wannan tilawa ta karshe ce za a saurari ra’ayin jama’a a kan kudirin dokar, wadda aka shafe shekaru ana sa-toka-sa-katsi a kan ta.

Idan wannan kudiri ya zama doka dai kenan za a rushe duk wasu hukumomin kula da harkokin man fetur, da su ka hada da NNPC da PPPRA.

Bayan rushe Hukumar NNPC, wannan doka za ta bada iznin kafa Kamfanin National Petroleum Corporation Limited.

Kudirin Dokar kuma zai bada damar kafa wasu kamfanonin kula da bangarorin fetur guda biyu.

Monguno ya ce akwai bukatar hanzarta ganin kudirin PIB ya zama doka, domin nan da shekaru 25 harkar hako danyen mai za ta gurgunce.

“Ba wai cewa na yi za a daina hako danyen mai nan da shekaru 25, ko kuma danyen mai zai kafe ba. A’a, ina nufin yanzu duniya ta ci gaba saboda ana ta bijiro da hanyoyin cin moriyar makamashi a saukake a duniya. Kuma hanyoyin da ake ta bijiro da su, sun fi sauki matuka fiye da amfani da sinadaren fetur.” Inji shi.

Tun cikin 2008 ake ta tsallen-badaken kokarin ganin an kafa dokar kudirin PIB, amma abu ya faskara.

Idan ba a manta ba, ko lokacin da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ke kamfen a zaben 2019, sai da ya ce idan ya ci zabe zai sayar da NNPC.

Share.

game da Author