Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 198 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Laraba.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Laraba sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –48, FCT -53, Ogun-40, Akwa Ibom-20, Bauchi-9, Filato-8, Kaduna-5, Kano-4, Benue-3, Jigawa-3, Nasarawa-3, Edo-1 da Kwara-1
Yanzu mutum 66,805 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 62,493 sun warke, 1,169 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 3,143 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 23,066, FCT –6,629, Oyo – 3,715, Edo –2,696, Delta –1,823, Rivers 2,963, Kano –1,781, Ogun –2,196, Kaduna –2,945, Katsina -1,012, Ondo –1,727, Borno –745, Gombe – 938, Bauchi – 762, Ebonyi –1,055, Filato -3,813, Enugu – 1,332, Abia – 926, Imo –662, Jigawa – 331, Kwara –1,096, Bayelsa – 445, Nasarawa – 488, Osun –945, Sokoto – 165, Niger – 296, Akwa Ibom – 339, Benue – 496, Adamawa – 261, Anambra – 282, Kebbi – 93, Zamfara – 79, Yobe – 94, Ekiti – 354, Taraba- 157, Kogi – 5, da Cross Rivers – 90.
Zuwa yanzu alkaluma sun nuna cewa sama da mutum miliyan biyu sun kamu da cutar a Nahiyar Afrika
Mutum sama da miliyan 1.7 sun warke sannan mutum 48,000 sun mutu a dalilin kamuwa da cutar.
Ofishin WHO dake Brazzaville kasar Kongo ya sanar da haka.
Kasashen Afirka ta Kudu, Algeria da Kenya ne kasashe a nahiyar da suka fi kamuwa da cutar.
Kasar Afrika ta Kudu mutum 757,144 sun kamu, 20,556 sun mutu.
A Algeria mutum 70,629 sun kamu, 2,206 sun mutu.
Kasar Kenya ta samu mutum 72,686 da suka kamu da mutum 1,313 da Suka mutu