Ma’aiakatar Harkokin Noma ta rika yin amfani da maimaita biyan kudi sau biyu, bad-da-bamin lissafi da ‘yar-burum-burum wajen karkasa naira bilyan 3.08 cikin asusun wasu ma’aikatan ta, abin da karara ya karya dokar tasarifin kudade ta kasar nan, wadda ta haramta tura kudaden gwamnati aljihun ma’aikacin gwamnati.
Kamar irin yadda Ma’akatar Makamashin Lantarki ta yi na ta watandar a jajibirin karshen shekarar 2019, ita ma Ma’aikatar Harkokin Noma a karkashin Minista Sabo Nanono, ta yi wa na ta ma’aikata su 42 watandar naira bilyan 3.08 a jajibirin karshen 2019. PREMIUM TIMES ta tabbatar da an tafka wannan gurungunduma, kuma akwai kwafe-kwafe na takardun bayanai masu shaida haka.
An rika karkatar da kudaden ta hanyoyin bad-da-bamin lissafi da ‘yar-burum-burum wajen karkasa naira bilyan 3.08 cikin asusun wasu ma’aikatan ta, abin da karara ya karya dokar tasarifin kudade ta kasar nan, wadda ta haramta tura kudaden gwamnati aljihun ma’aikacin gwamnati.
An Dankara Wa Wata Mata Naira Milyan 255.35, Ba Cas Ba As:
Cikin wadanda aka fi zabga wa kudade akwai wata mata mai suna Zainab Bala, wadda aka kamfato naira milyan 255.35 aka maka cikin asusun ajiyar ta na banki.
Sai kuma wani mai suna Mohammed Lawan, shi ma ya taki sa’a, ta take da naira milyan 246.3.
An ce naira milyan 81 daga cikin kudin da aka dankara wa Mohammed Lawan, na shirya taro ne na 44 na Ma’aikatar Gona da Raya Karkara a Jos. Amma kuma kamata yay i a tura wa ‘yan kwangila kudaden kai-tsaye, ba sai sun bi ta asusun Mohammed Lawan ba, wanda ma’aikaci ne a ma’aikatar.
Ita kuma Zainab, sau biyu aka tura kudi asusun ta. Na farko naira milyan 125, sai karo na biyu naira milyan 130. An rattaba cewa kudaden duk na fara aiki ne a sabuwar Jami’ar Noma ta Gwamnatin Tarayya ta Zuru, Jihar Kebbi.
A cikin wannan watan dai an sake zabzar naira milyan 100 aka tura wa wata mata mai suna Aisha Ahmed da kuma wani Dipnap Nandom shi kuma naira milyan 145. Abin mamaki, sai aka rubuta cewa aikin da aka tura kudi asusun Aisha Bala za a yi da kudin. Wato an biya kudin sau biyu kenan.
GA YADDA AKA KASAFTA KUDADEN, KOWA YA YI GUM DA BAKIN SA
LAMBA: SUNAN MA’AIKACI KUDIN DA AKA TURA MASA
1 ZAINAB BALA 255,350,000
2 MOHAMMED LAWAN 246,298,032
3 NDAKOTSU, MRS. AMINA 174,290,679
4 EBEBI GEORGINA SADIA 172,081,056
5 ABDULRAHMAN, MR. IBRAHIM 171,397,600
6 DIPNAP, MR. NANDOM STEPHEN 145,000,000
7 IJAOBA MUSILIMAT OLAMIDE 140,630,792
8 AJUNWA TOCHUKWU GODWIN 132,114,150
9 AHMED, MR. ARIBO HUSSEIN 126,102,800
10 ONUH OJO SALOME 120,150,201.72
11 ANYAELE, MR. CHARLES OGBONNAYA 107,077,013.85
12 AISHA AHMED 100,000,000
13 MAIMUNA EBILOMA 96,992,000
14 RAUF, MRS. SILIFAT IBIDUNNI 92,985,000
15 ASAAGA BEM 88,299,464.11
16 OKUGO, MRS. STELLA CHINYERE 87,000,000
17 HABIBA SALIHU USMAN 77,337,000
18 EBHOHIMEN, MR. ASEGBE MONDAY 71,466,400
19 NWOKEDI, MRS. PATRICIA EBELE 60,362,000
20 EBENJE, MRS. GLORIA UDOKA 58,614,521
21 KUTEYI BOLA ALEX 54,088,706
22 PAM, MR. GABRIEL MARCELLINUS 50,000,000
23 BANJO, MR. SUNDAY JOHN 49,783,200
24 PETER-OKPO, MS. VERA MMAOBONG 46,566,000
25 DAFUNG, MR. YILPRING IBRAHIM 39,393,767
26 ADAMS, MR. . JOSHUA 32,585,943
27 EGWIM, MRS. OZIOMA STELLA 28,715,400
28 JOEL OYETUNJI AKINADE 24,915,979
29 EGBUNU ALADI DORA 24,700,000
30 EDOGBO, MR. SULE 23,534,500
31 UMAR, MR. MOHAMMED SALISU 22,809,000
32 AVIDIME, MS. EWEZE ELIZABETH 21,589,200
33 DIKE AMECHI OTUYA 21,345,614.43
34 IBRAHIM, MR. MOHAMMED 20,626,826.6
35 ADEBIMPE, MRS. OLUWASOLA ESTHER 18,025,159.05
36 ADEBAYO OLORUNTOBI 16,221,750
37 LINUS S E R EYITIMI 14,677,900
38 SULEIMAN, MR. IBRAHIM 14,581,202
39 AKINFOLARIN KUTI, MRS. KATE OLUWATOYIN 10,165,000
40 ONYEDINEFU, MRS. CHIOMA VIRGINIA 9,955,975.78
41 AROKE, MRS. AMORE GRACE 9,109,200
42 ABDULMALIK, MR. WALI SANI 7,900,777.08
JIMILLA: NAIRA 3,084,839,809.62