Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari saboda agajin gaggawa da ya kai wa al’ummar jihar sakamakon bala’in ambaliyar ruwan sama da aka yi a jihar.
Ambaliyar ta shafi kananan hukumomin Gwadabawa, Illela, Sokoto ta Arewa, Wammako, Bodinga da Tambuwal, inda ta lalata gonaki da amfanin gona masu yawan gaske.
Gwamnan ya yi yabon ne a karshen makon jiya lokacin da Ministar Harkokin Jinkai, Agaji da Inganta Rayuwa, Sadiya Farouq, ta ziyarci jihar domin rarraba kayan agaji tare da kaddamar da Shirin Bada Lamuni Ga Matan Karkara, wato ‘Rural Women’s Grant Project’.
Ya ce: “Tilas ne in yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari saboda sakon alheri, jajantawa da tausayawar da ya yi mana tun farko a kan bala’in da ya faru a garuruwan mu masu yawa, da kuma tallafin da ya ba wadanda abin ya shafa.
“Mu na aikin fito da wani kasafin kudi na musamnan da za mu kai wa Shugaban Ƙasa don ya ga yadda za mu sake gina gidaje, asibitoci da makarantu da ambaliyar ta shafa.
“Mu na kuma yaba wa mai girma Shugaban Kasa saboda ayyukan sa na agaza wa jama’a. Akwai su da dama kuma mu na godiya kan yadda Jihar Sokoto ta amfana daga wadannan shirye-shirye.
“Mu na tabbatar maku da cewa al’umma da gwamnatin Jihar Sokoto a shirye mu ke mu hada gwiwa da ku a kowane shiri da zai amfani jama’a.”
Gwamnan, wanda ya bayyana Jihar Sokoto a matsayin jiha mai tanyon mata, ya yi alkawarin kara azama wajen karfafa wa mata, musamman wadanda ke zaune a yankunan karkara.
Tun da farko, sai da Minista Sadiya ta jajanta wa gwamnatin jihar a kan bala’in ambaliyar.
Ta ce, “Mai Girma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya damu da barnar da ambaliyar ta jawo kuma ya bada umarni ga Ma’aikar Harkojin Jinkai, Agaji da Inganta Rayuwa ta Tarayya da ta sa Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta yi azama wajen samar da taimakon da mutanen da abin ya shafa ke bukata. Ga ni na zo tare da Darakta Janar na NEMA domin mu kawo kayan agaji da aka amince a rarraba don taimakon wadanda abin ya shafa.”
Kayan agajin da aka kai wa jihar sun hada da buhun masara 1,502, buhun shinkafa 1,502, buhun wake 1,502, garwar manja 107, garwar man girki 43, katan-katan na kayan hadin girki guda 202, katan 141 na tumatirin gwangwani da kuma buhu 22 na gishiri.
Sauran sun hada da bargo 3,868, katifa 3,868, gidan sauro 3,004, buhun siminti 3,780, bandir din kwanon rufi 3,780, buhun kusa 723, fakitin kusar kwano 200 da kuma katan 72 na omo.
Ministar ta yi la’akari da cewa tun ma kafin a raba wadannan kayan agajin, Gwamnatin Tarayya ta riga ta tura wasu kayan agajin ga al’ummar Ƙaramar Hukumar Goronyo da ambaliyar ta shafa, ta hanyar NEMA.
Ta ce, “Ofishin NEMA da ke Sokoto ya gudanar da binciken gani da ido a kananan hukumomin Binji da Silame. An amince a kai masu kayan agaji kafin karshen satin nan kamar haka:
i. buhun shinkafa 455 (kilo 12.5)
ii. buhun masara 455 (kilo 12.5)
iii. buhun wake 455 (kilo 25)
iv. katan 76 na kayan haɗin girki 76
v. jarka 46 (lita 20) ta man girki
vi. katan 38 na tumatirin gwangwani
vii. bargo 910
viii. katifa 910
ix. gidan sauro 910
x. buhun siminti 600
xi. bandir 600 na kwanon rufi
xii. fakiti 200 na kusar kwanon rufi
xiii. buhu 67 na ƙusa inci 3
Za A Rika Biyan Naira 5,000 Ga A Gidaje 3,465 A Sokoto:
Sadiya ta kuma bayyana cewa za a rika biyan N5,000 a kowane wata ga gidaje 3,465 na mabukata a Jihar Sokoto, yayin da ana shirin rubuta gidaje 29,676 na mabukata cikin wannan shirin.
Ta yi kira ga gwamnan da ya taimaka wa jihar domin ta shigar da karin mutane cikin shirye-shiryen bada tallafin da ma’aikatar ta ke gudanarwa.
Discussion about this post