#EndSARS: EFCC ta tabbatar cewa masu kutse sun afka cikin shafin hukumar ta intanet

0

Hukumar EFCC ta tabbatar da cewa manyan kadangarun bariki masu kutsen satar bayanan sirri a shafukan bayanan hukumomin gwamnati a duniya, sun kutsa cikin shafin hukumar a cikin ranakun Asabar da Lahadi.

Gungun wasu fitinannun masu kutse da ke kiran kan su ‘Anonymous sun yi ikirarin cewa su ne su ka fasa shafin, su ka shiga da karfin tsiya, domin nuna goyon bayan su ga zanga-zangar #EndSARS.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda wadannan kadangarun bariki su ka kwace shafin Babban Bankin Najeriya (CBN), Hukumar ‘Yan Sanda ta Kasa (NPF) da kuma Hukumar Zabe ta Kasa (INEC).

Tun a ranar Juma’a aka kutsa cikin shafin kamar yadda EFCC ta yi bayani cewa shafin na ta na intanet ya kasance a kulle, babu halin shiga.

A ranar Litinin EFCC ta sanar cewa daga baya ta kwato shafin, kuma ta fatattaki ‘yan kutsen daga cikin shafin ta.

“An Yi kokarin kutsawa, har ma shafin ya yini a kulle. Amma yanzu mun Yi nasarar korar su, mun kuma samu nasarar kwato shafin, yanzu haka ya na ci gaba da aiki.

“Mu na jan hankalin kowa ya yi watsi da rahotannin cewa an kwace mana shafin intanet. Ya na hannun mu, kuma yanzu haka ya na ci gaba da aiki.

EFCC ta kuma karyata rahotannin da ke cewa wani jami’in ta ya ajiye aiki domin nuna goyon baya ga masu fafufikar a yi wa aikin ‘yan sanda garambawul.

Ta ce wani dan bautar kasa (NYSC) da ya kammala aikin bautar kasa a ofishin EFCC da ke Fatakawal ne, amma ba ma’aikacin EFCC ba ne.

Share.

game da Author