RASHIN TSARO: Dalilin da ya sa Najeriya ba ta samun dauki daga kasashen Turai – Aminu Wali

0

Tsohon Ministan Harkokin Waje, Aminu Wali, ya bayyana dalilin da ya sa manyan kasashen duniya ba su kawo wa Najeriya dauki wajen yaki da Boko Haram.

Wali ya taba zama Wakilin Dindindin na Majalisar Dinkin Duniya, kuma shi ne Ministan Harkokin Waje tsakanin 2014 zuwa 2015, lokacin rubdugun hare-haren Boko Haram.

Da ya ke amsa tambaya daga PREMIUM TIMES, Wali ya ce gwamnati kan yi asarar rashin samun dauki daga manyan kasashen duniya, sau da yawa saboda yanayin irin adawar da ‘yan adawa ke wa gwamnati a cikin gida.

Ya ce kasashen duniya sun fi gaskata kalaman masu adawa da gwamnati, wadanda kan haddasa toshe wa kasa wasu damammaki, hana ta wasu dauni da kuma kakaba mata takunkumi zuwa maida ta ware-ga-dangi.

Ya ce irin wannan misalin ya faru a lokacin da ya ke Ministan Harkokin Waje.

“Idan ana maganar tsaro, to su jam’iyyun adawa sun fi bada karfi wajen caccakar gwamnati, ba ta hanyar bada shawara da goyon baya ba.”

Ya ce to kasashen Tuwai sun sha rungumar soke-soken da masu adawa ke yi na farfaganda a lokacin mu, har mu ka shiga matsala da su.

“Misali, mun nemi helikwafta kirar Cobra daga Amurka. Amma a lokacin ina Ministan Harkokin Waje su ka ki sayar mana. Daga nan mu ka doshi Turkiyya. Su ka ce za su sayar mana, amma matsalar, injin din na su helikwafta din, na kasar Amurka ne. Don haka sai sun nemi lasisi daga Amurka tukunna. Ita kuma Amurka ta ki maida hankali wajen bayar da lasisin.” Inji Wali.

Ya sake bada labarin yadda su ka kwaranye da jami’an difilomasiyyar Amurka, lokacin da Goodluck ya dage zaben 2015 da wata daya.

Wali ya ce duk da an shaida wa Amurka cewa an yi hakan ne saboda matsalar tsaro, amma su hankalin su ya fi karkata da son a samu canjin gwamnati, maimakon su taimaka wa Najeriya a dakile matsalar tsaro.

Share.

game da Author