Mahara da akalla sun kai su 100 ne suka dirawwa ofishin ‘Yan sanda dake Gidan Madi, karamar hukumar Tangaza, Jihar Sokoto.
Kakakin rundunar ‘Yan sandan jihar Sokoto, Muhammed Sadiq ya bayyana cewa maharan da suka kai su 100 sun dira wannan kauye da misalin kafe 1:30 na dare sannan suka afkawa ofishin ‘yan sandan.
Sadiq ya ce mutum biyu aka rasa bayan batakashi da jami’ai suka yi da mahara.
Cikin wadanda aka kashe akwai DPO Aliyu Bello da Sufeto daya mai suna Muhammad Abdullahi sannan jami’i daya mai Sani Abdullahi ya samu rauni a jikin sa.
Sadiq ya kara da cewa kwamishinan ‘Yan sandan jihar Ibrahim Kaoje ya bayyana rashin jin dadin sa kan abinda ya faru yana mai cewa tabbas za a gudanr da bincike akai sannan za adau mataki akai.