Jarumin finafinan Kannywood dana Nollywood Yakubu Mohammed, ya yi dana sanin fitowa a wani fim na ‘yan kudu da aka dauke shi a Enugu kan ‘yan shia.
Yakubu ya ce da ya sani da bai yarda ya fito a wannan fim ba.
A hira da yayi da BBC Hausa ya bayyana rashin jib dadin sa da kuma kokari da yayi na ganin an cire shi a fim din bayan an kammala daukar sa.
‘Yan Shi’a a fadin kasar nan, karkashin IMN, sun yi Allah wadai da yadda aka nuna su a fim din ‘Fatal Arrogance’, cewa su ‘yan ta’adda ne.
Sun kuma yi tir da babban jarumin fim din, Pete Edochie, wanda ya fito a matsayin El-Zakzaky, a fim din wanda aka shirya a Enugu.
Duk da fim din bai fito ba, amma dai wani tsakuren minti 12 da aka watsa ya haifar da tashin jijiyoyi sosai a soshiyal midiya.
IMN ta ce fim din farfaganda ce ta bata sunan ‘yan Shi’a da kuma jagoran su Sheikh Ibrahim Zakzaky.
Cikin wata takardar manema labarai da Kakakin IMN, Ibrahim Musa ya turo wa PREMIUM TIMES HAUSA, mai dauke da sa hannun sa, ya ce:
“A ranar 9 Ga Satumba, 2020, wasu gajerun bidiyoyi na fim mai suna “FATAL ARROGANCE”, wanda Furodusa Anosike Kingsley Orji ya shirya a birnin Enugu suka karade shafukan sada zumunta na intanet, inda a ciki aka rika nuna mata ba suturar kirki, kamar wasu matsafa, rirrike da takubba da adduna da kwalaye da hotunan wani malami cikin rawani, su na kuma furta wasu kalmomi marasa ma’ana da sunan su na yin muzahara.
“Hakika mun kadu da ganin cewa a fim din ana kokarin kamanta Harkar Musuluncin da Jagoran ta Shaikh Ibraheem Zakzaky a matsayin ‘yan ta’adda.
“Da a ce ba wata a kasa, irin wadannan gajerun bidiyon za mu iya yin biris da su, amma ba a a irin wannan hali da gwamnatin Buhari ta ke daukar nauyin ‘yan kwangila masu yin batanci, musamman mutum irin Kuanum Terrence, wanda kowa ya san rundunar sojar Nijeriya ta dauke shi aikin yi mata farfaganda a kan bata harkar Musulunci, wacce aka san ta a tsawon shekaru da kauce wa tashin hankali duk da hare-haren takala da ake kai mata.
“A sarari ya ke ga kowane dan kasa cewa wadannan gajerun bidiyon manufarsu ita ce shafa wa Harkar Musulunci kashin kaji da nuna ta a matsayin wata Harkar tashin hankali da ta’addanci a idon duniya. Har ila yau wannan fim din da ake daukar sa a halin yanzu sunan sa ya yi daidai da littafin da Terrence ya wallafa a bara, wanda bisa kudurar Allah bai samu karbuwa ba a gun jama’a, inda a ciki aka zargi wadanda aka zalunta da jawo wa kan su zalunci. Sunan littafin da Hausa wai “Mugun taurin kai: Yadda El-Zakzaky ya rudi ‘yan Harkar Musulunci su ka kashe kan su yayin kare shi”. Daga sunan littafin ma, wautar da ke cikin sa ta bayyana a sarari.”
Ya kubu ya kara da cewa ya har kudi ya nemi ya baiya wadanda suka shirya fim na hasara da zasu yi, amma basu ce komai ba.
” Wato lokacin da aka kawo min rubutaccen labarin fim din na duba, sai na ga labari ne a kan abin da ya faru a Zaria tsakanin kungiyar Muslim Brothers da sojoji, inda aka karkashe kuma aka harbi ‘yan kungiyar ‘Yan uwa Musulmin. To da aka kawo min script din, har ga Allah ban taba sanin cewa akwai wani littafi ko rubutu da aka yi mai wannan sunan na “Fatal Arrogance” ba.
” A gaskiya na yi da-na-sani saboda da farko na shiga ne da da kyakkyawar niyya amma yadda abubuwa suka kasance na ka ji ba dadi.
” Wani zai kira ka ya ce ‘Haba Mallam Yakubu, me yasa ka fito a haka?’ To ita harkarmu ta fim ka kan iya fitowa a boka, ka kan iya fito wa a malami, kuma za ka iya fitowa a dan sanda.