Gwamnati kasar Amurka ta yi wa ‘yan kasanta da ayyuka a Najeriya da zama da su gargadin cewa kada su kuskura su rika garzayawa jihohi kamar su Kaduna, Kano, Barno, Bauchi da dai sauran wasu jihohin Najeriya cewa hakan yana da hadarun gaske.
Amurka ta wallafa wadannan bayanai na gargadi da jan kunne a shafinta dake a yanar gizo tana mai cewa jihohi da dama a Najeriya sun zama shiga da alwalanka wato akwai yiyuwar ka fada tarkon ‘yan ta’adda.
Amurka ta ce saboda garkuwa da mutane da ake yi a jihohi irin su Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Kaduna, Kano, da Yobe, tana jan kunnen yan kasar ta su kaurace wa wadannan jihohi.
Haka kuma ta shaida cewa suma jihohin kudancin Najeriya ba wurin zuwa bane ga ‘yan kasan ta.
Ta lissafo jihohi kamar su Akwa Ibom, Bayelsa, Cross Rivers, Delta, da Rivers a matsayin jihohin da ba za ta ba mutanen kasarta shawara su je ba. ” Ku kaurace wa wadannan jihohi.
Sai dai kuma duk da matsalar tsaro da ake fama da shi a kasar nan shugaba Muhammadu Buhari a cikin wannan mako ya yabi irin namijin kokarin da manyan hafsoshin Najeriya su ke yina ganin sun murkushe ‘yan ta’adda, masu garkuwa da mutane da mahara.
Idan ba a manta ba kasar Amurka a ranar Alhamis ta shaida cewa kungiyar A-Qidah
na kutsuwa cikin Najeriya, ya kin Arewa Maso Yamma.