An kara makonni hudu a wannan babi na sassaucin Korona da ake ciki – Kwamitin Korona

0

Gwamnatin tarayya ta kara mako hudu bisa tsarin babi na biyu na sassauta dokokin Korona a kasar nan.

Sakataren gwamnati kuma shugaban kwamitin shugaban kasa kan dakile yaduwar cutar Covid-19 Boss Mustapha ya sanar da haka a Abuja ranar Alhamis.

Mustapha ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da haka sannan ya ce za a ci gaba da sassauta dokar bayan karin makonni 4 da gwamnati ta yi.

Ya ce gwamnati za ta ci gaba da hada hannu da sauran sassan gwamnati da hukumomin kiwon lafiya domin dakile yaduwar cutar covid-19.

Sannan ta kuma yi kira ga mutane da su ci gaba da kiyaye sharuddan guje wa kamuwa da cutar domin samar wa kansu kariya da Lafiya.

Yanzu mutum 44,890 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 32,165 sun warke, 927 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 11,798 ke dauke da cutar a Najeriya.

Idan ba a manta ba a ranar 27 ga watan Afrilu ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya fara sassauta dokar Hana walwala a jihohin Legas da Ogun da Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Daga ranar 4 ga watan Mayu, aka ci gaba da walwala tun daga karfe 9 na safe zuwa karfe 8 na dare, daga nan kuma za a shiga kulle sai safiyar gobe.

Daga nan Kuma a ranar 27 ga watan Yuli Mustapha ya sanar cewa gwamnati ta kara mako daya bisa tsarin babi na biyu na sassauta dokar hana walwala a kasar nan.

Ya ce mako dayan da gwamnati ta kara zai fara ranar 29 ga watan Yuli zuwa 6 ga watan Agusta.

Mustapha ya ce gwamnati ta yi wannan karin ne domin kare kiwon lafiyar mutane daga cutar Korona a wannan lokaci da ake tunkarar bukukuwan Babban Sallah.

Yanzu kuma sai an sake safe makonni hudu tukunna kafin asan wani layi gwamnati ta dauka ko za asaki komai ko kuma dai za a cu gaba da zama haka ne.

Share.

game da Author