HADARIN JIRGIN RUWA: Mutum 9 sun rasu a Sokoto

0

Rundunar ‘Yan sandan jihar Sokoto ta sanar da rasuwar wasu mutane su tara sanadiyyar hadarin jirgin ruwa da aka yi a kauyen Birjingo dake Karamar Hukumar Goronyo.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar Muhammad Sadiq wanda ya tabbatar da haka wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Alhamis ya ce hadarin ya auku ranar Laraba.

Sadiq ya ce rundunar na gudanar da bincike domin gano adadin yawan mutanen dake cikin jirgin a lokacin da hadarin ya auku.

“Banda mutanen da aka ceto dake jirgin an tsamo gawar mutum shida.

Mai rikon kwaryan shugabancin karamar hukumar Goronyo Zakari Shinaka ya ce hadarin na faruwa ya aika da mutum 50 domin ceto mutanen da jirgin ruwan ya kife da su.

Shinaka ya yi kira ga masu daukan mutane a jirgin ruwa da su daina dankara mutane fiye da yadda jirgin zai iya dauka mutane cewa yin haka ne ke kawo matsalar kifewar jirgi a ruwa.

Ya Yi wa iyalen mutane shida da suka rasu a hadarin kuma ya umurci masu unguwanni da suka damke duk wani mai mallakin jirgin ruwan da aka dankarashi da mutane fiya da adadin da ya kamata ya dauka.

Wani mutum da hadarin ya auku a idon sa ya bayanai cewa jirgin ruwan ya dauko mutum sama da 30 a lokacin da hadarin ya auku.

Ya ce mafi yawan mutanen da ke jirgin manoma ne Kuma ‘yan kwadago dake aiki a Wani gona dake tsallaken wannan Rafi.

Share.

game da Author