Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Sanusi Lamido Sanusi, ya bayyana cewa daurar wadanda ba su cancanta ba a dora kan manyan mukamai ne tushen cin hanci da rashawa a Najeriya.
Sanusi ya yi wannan bayani ne a wani taro da ‘Emmanuel Chapel’ ya shirya a ranar Juma’a, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Sanusi ya ce bayar da mukamai ga mutane ta hanyar wanda su ka sani, ko alakar abota, ‘yan’uwantaka da kuma kusanci, ba zai kai Najeriya gaci ba.
Masu sukar Shugaba Muhammadu Buhari na ci gaba da matsa-lambar cewa nade-naden da ya ke yi musamman a bangaren shugabancin tsaro duk kabilanci da bangaranci ne, domin bai yi la’akari da sauran bangarori da kabilun yankunan kasar nan daban-daban ba.
Tsarin dauka aiki da nade-naden manyan mukamai da ke cikin kundin dokar Najeriya tun ta 1979, ya jaddada yin adalci tsakanin bangarori, shiyya da kabilun kasar nan, wajen nade-naden mukamai da daukar manya da kananan ma’aikata.
“A addinance ma rashawa da cin hanci babbar matsala ce. Amma bari mu fara kallon abin ta fuskar tattalin arziki tukunna.
“Daga cikin matsalolin akwai nada mukamai ga wadanda ba su cancanta ba. Don haka a koda yaushe nake cewa a a rika bin tsarin da Gwamnatin Tarayya ta gindaya wanda ke shimfide a cikin doka, yadda kowane dan bangare zai shiga a tsarin, amma fa a bisa cancanta.
“Mummunan cin hanci da rashawa da yafi damun kasar nan, shi ne kabilanci da bangaranci, ta yadda ake raba mukamai ta hanyar sanayyar kabila ko kusancin dangantaka da kuma bangaranci da shiyyanci da abokantaka. Maimakon a rika daukar wadanda suka cancanta ana nada su mukaman.
“Saboda haka mu na bukatar mutanen da za su ceto Najeriya daga hannun ‘yan jagaliya. Ina maganar wadanda za su ceto Najeriya gaba daya.”