Buhari ne ke rike da akalar mulkin kasar nan gam-gam -Fadar Shugaban Kasa

0

Fadar Shugaban Kasa ta fitar da sanarwar da ke matsayin maida raddi, ta na cewa Shugaba Muhammadu Buhari ne ke rike da ragamar mulkin Najeriya gam-gam.

A cikin wata sanarwa da Kakakin Yada Labarai na Fadar Shugaban Kasa, Garba Shehu ya fitar a ranar Lahadi, ya bayyana rubuce-rubucen da ake yi a kafafen yada labarai masu nuna cewa ragamar mulki ta subuce wa Buhari, Garba ya ce kirkirar karairayi ne kawai da rashin nemar wa kasar nan alheri da wasu ke rubutawa.

“Ai watsa irin wadannan munanan kalamai a kafafen yada labarai ya kara tabbatar da cewa akwai ‘yancin fadin albarkacin baki ga kowa a kasar nan.” Inji Garba Shehu.

Ya kuma kara bayyana a gidan talbijin na Channels ya kara jaddada wannan batu.

Ya ce akwai wasu kura-kurai da kuma aikata ba daidai ba da wannan gwamnati ke bincikowa kuma ta na magance su, ba tare da sun janyo wa kasar zubewar kima ba.”

Shehu ya yi kaca-kaca da masu rubuce-rubucen cewa ba Buhari ne rike da akalar mulkin Najeriya ba.

“Wasu lokutan mu na mamakin irin yadda wasu masu rubuce-rubucen nan ba su yin taka-tsantsan cewa abin da suke rubutawa na da illoli ga kasar nan, daga cikin ta da kuma wajen kasar.

“Ko batun Ibrahim Magu ko batun Godswill Akpabio, NDDC ko NISTF, ko ma wane batu, ‘yan Najeriya na da ‘yancin fadar ra’ayin su, kamar yadda dokar kasar nan ta bayar.

“Amma abin tayar da hankalin shi ne sai ka ga wasu sun takarkare su na rubuce-rubucen da kai da gani ka san yawun ‘yan adawa ne a cikin alkalamin su, wadanda su ne dai a cikin shekaru 16 suka durkusar da kasar nan.”

Shehu ya yi tsokaci a kan masu sukar binciken NDDC da NISTF da sauran su a karkashin mulkin Buhari, ya na mai cewa sun manta tun daga gwamnatocin baya aka fara binciken. Wadanda kuma gwamnatin da ta gabata ba ta yi komai a kai ba.

Ya ce har yau har kuma gobe ragamar mulki a hannun Buhari ta ke, kuma ya nan kan bakan sa na yin riko da rantsuwar da ya dauka domin ya tabbatar da yin adalci wajen dakile wadannan batutuwan wawurar makudan kudade a kasar nan.

Share.

game da Author