Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 556 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Lahadi.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Lahadi sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum –97, Edo-104, FCT-70, Benue-66, Oyo-61, Kaduna-38, Filato -28, Osun-19, Akwa Ibom-14, Rivers-13, Katsina-13, Ondo-13, Ogun-6, Kano-5, Nasarawa-4, Gombe-2, Ekiti-2 da Borno-1.
Yanzu mutum 36,663 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 15,105 sun warke, 789 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 20,769 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 13,438 FCT – 3,027, Oyo – 2,167, Edo – 1,989, Delta – 1,423, Rivers – 1,529, Kano – 1,400, Ogun – 1,174, Kaduna – 1,156, Katsina –710, Ondo – 925 , Borno –599, Gombe – 546, Bauchi – 529, Ebonyi – 655, Filato – 648, Enugu – 675, Abia – 497, Imo – 452, Jigawa – 322, Kwara – 535, Bayelsa – 322, Nasarawa – 276, Osun – 351, Sokoto – 153, Niger – 151, Akwa Ibom – 175, Benue – 260, Adamawa – 115, Anambra – 118, Kebbi – 88, Zamfara – 77, Yobe – 64, Ekiti – 86, Taraba- 30, Kogi – 5, da Cross Rivers – 13.
Matakan da Zamfara ta dauka wajen dakile yaduwar Korona a jihar
Kakakin gwamnan jihar, Zailani Bappa ya bayyana matakan da gwamnatin jihar ta dauka da ya sa aka samu nasarar dakile yaduwar cutar a jihar.
1 – Gwamnati Zamfara ta bi dokar gwamnatin tarayya sauda kafa tun da farkon bullowar cutar a kasar nan.
Mun rufe makarantun mu tunda wuri, mun rufe kasuwanni da iyakokin jihar mu, sannan mun saka dokar kowa ya saka takunkumin fuska dole-dole. Mun yi haka ne tun kadin cutar ta dira jihar mu ma.
2 – Kafin cutar ta bulla a Zamfara gwamtai ta kafa kwamiti biyu, daya domin wayar da kan mutane game da cutar dayan kuma domin basu tallafi
3 – Mun wadata wuraren da aka kebe domin kula da wadanda suka kamu da cutar a jihar. Mun samar da kadajen marasa lafiya akalla 100, na’aurar shakar iska, na’urar yin gwajin jutar da takunkumin fuska.
4 – kun yi wa kasuwanni feshin magani, makarantu da cikin gari baki daya.
5 – Ko a loacin da ake ta kokarin maidsa Almajirai jihohin su na asali, na mu da aka dawo da su sai da muka yi musu gwaji kafin suka shigo cikin gari.