Gwamnatin Tarayya za ta kara narka naira bilyan 108 domin kammala wasu titina a kasar nan -Fashola

0

Gwamnatin Tarayya ta amince za ta kara narka naira bilyan 108 a kan yadda aka rigaya aka kasafta kudaden ayyukan kwangilolin wasu titina, domin a samu damar karasa ayyukan gina su.

Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola ne ya bayyana haka, ranar Laraba, a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a Fadar Shugaban Kasa.

Ya yi bayanin ne jim kadan bayan kammala taron mako-mako na Majalisar Zartaswa, wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta.

Fashola ya ce an amince a kara narka wa ayyukan titinan wadannan makudan kudade domin a samu sararin kammala su.

Daga cikin titinan da za a kara narka kudaden a kan su, akwai:

1. Kammala aikin babban titin da ya tashi daga Enugu zuwa Fatakwal, wanda aka amince a kara wa naira bilyan 25 domin a kammala shi.

2. Narka wasu kudade har naira bilyan 60 domin kammala aikin titin da ya tashi daga Dikwa zuwa Marte zuwa Monguno.

3. Kara narka naira bilyan 15.527 domin kammala titin Monguno zuwa Numan.

4. Za a kara narka naira bilyan 7.643 domin kammala titin Gombi zuwa Biu.

Baya ga titin da ya tashi daga Enugu zuwa Fatakwal, sauran titinan duk a cikin Jihar Barno da Adamawa suke.

Share.

game da Author