Babbar Kotun Tarayya da ke Asaba, ta yi fatali da rubutaccen rokon da Hukumar SSS suka shigar a gaban ta, inda suka roki kotun ta jingine hukuncin tilasta su biya diyyar naira milyan milyan 10 ga wani Anthony Okolie.
Kotu ta tuhumi SSS da danne wa Okolie hakkin sa ta hanyar tsare shi tsawon lokaci, ba tare da gurfanar da shi kotu da wuri ba.
Lauyan Okolie ya shigar da kara ne bayan an kama Okolie ana zargin sa da mallakar wani tsohon layin wayar MTN da Hanan, ‘yar Shugaba Muhammadu Buhari ta taba amfani da shi.
Okolie ya ce shi dai sayen layin ya yi a kamfanin MTN. Daga nan ya maka Hanan, SSS da MTN a kotu saboda cin zarafin sa da aka yi, alhali MTN din da kan su suka sayar masa da layin.
Mai Shari’a Nnamdi Dimgba ya yi fatali da bukatar SSS, ya ce alkalami ya rigaya ya bushe, Babbar Kotun Tarayya ba ta da hurumin sauraren karar su, sai dai Kotun Daukaka Kara kadai.
Lauyan Okolie ya ce abin da SSS ke yi tsalle-tsallen da ba zai fisshe su ba ne. Ya ce zai sake shigar da karar lattin biyan kudin diyyar da SSS suka yi.
Lauyan ya ce zai ci gaba da hura wa hukumar wuta har sai ta biya wanda ta zaluntar hakkin sa.
Ranar Laraba PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin SSS sun daukaka karar cin su tarar naira milyan 10 da Kotun Tarayya ta yi.
Wannan jarida ta ce Hukumar Tsaro ta SSS ta daukaka karar hukuncin tarar naira milyan 10 da Kotun Tarayya ta yanka musu, bisa samun su da laifin tauye hakkin wani da ya sayi tsohon layin wayar MTN, mallakar Hanan Buhari, ‘yar Shugaba Muhammadu Buhari.
Cikin watan Mayu Premium Times ta buga labarin yadda Babban Mai Shari’a na Kotun Tarayya, Nnamdi Dimgba ya umarci jami’an SSS su biya Anthony Okolie diyyar naira milyan 10, saboda tsare shi na tsawon lokaci da suka yi ba da umarni daga kotu ba.
Kotun wadda ke da zama a Asaba, babban birnin jihar Delta, inda Okolie ya shigar da kara, ta ce abin da SSS suka aikata haramtacce ne, saboda babu shi a cikin tsarin kundin dokokin Najeriya.
Makonni kadan bayan yanke hukuncin, sai lauyan Okolie ya fara bibiyar SSS domin su biya naira milyan 10 din da kotu ta umarci su biya Okolie.
Sannan kuma lauyan Mai suna Tope Akinyode, ya yi barazanar sake maka SSS kotu, saboda sun raina kotu, ta hanyar yin biris da umarnin da kotun ta bayar cewa su biya naira milyan 10, tunda sun ki biya.
Ana cikin haka ne kuma sai SSS suka daukaka kara cewa ta na neman kotu ta dakatar da Okolie daga tirsasa hukumar cewa sai ta biya shi diyyar naira milyan 10 din.
PREMIUM TIMES ta tuntubj lauyan Okolie, ya kuma tabbatar da cewa tabbas SSS sun daukaka kara. Amma ya kara da cewa za su bi SSS har cikin kotu domin su kalubalanci karar da suka daukaka.
Kotu ta sa ranar 8 Ga Yuli domin jin ba’asin kowane bangare.