Babu rana ko lokacin biyan tsoffin sojoji cikon kudaden fanshon su na watanni uku – MPB

0

Hukumar Biyan Fanshon Tsoffin Sojoji ta bayyana cewa har yau ba ta aza rana ko lokacin fara biyan kudaden fanshon tsoffin sojoji na watanni uku da ba ta biya su ba.

Kakakin hukumar ta MPB, Olayinka Lawal ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai ranar Laraba.

Fitar da sanarwar ta biyo bayan ji-ta-ji-tar da ake watsawa a kafafen wasu jaridu cewa Hukumar Fanshon Tsoffin Sojoji ta aza ranar fara biyan kudaden.

Flight Laftanar Lawal ya ce, “Ana yada ji-ta-ji-tar Hukumar MPB ta tsaida ranar fara biyan tsoffin sojoji cikon kudaden su na watanni uku. Wannan ba gaskiya ba ce. MPB ba ta tsaida ranar fara biyan kudaden ba.

“Don haka aka jan hankalin masu karbar fanshon su yi kaffa-kaffa kuma kada su dauki ji-ta-ji-tar da muhimmanci, domin ba gaskiya ba ce.”

“Amma dai Shugaban MPB Manjo Janar Ahmadu Adamu da sauran mukarraban sa na aiki ba dare ba rana tare da hadin-guiwar hukumomin da suka kamata, domin ganin an kammala shirye-shiryen biyan da gaggawa.”

Lawal ya yi kira ga tsoffin sojojin su ci gaba da nuna goyon baya ga hukumar. Kuma su rika buga lambobin wayoyin da aka ba su, domin neman karin bayanin halin da ake ciki.

Share.

game da Author