Gwamnatin Kaduna ta bayyana cewa dakarun sojoji dake samar da tsaro a sassa dabam dabam na jihar sun garzaya tsaunin Zangan da wasu suka kawo rahotan cewa nan wani sansanin maboyar mahara ne da ke addabar mutane.
Wasu mazauna karamar Hukumar Kaura dake jihar Kaduna ne suka rika yada cewa sun gano wani maboyar mahara a tsaunin Zangang da ke afkawa mutanen da ke yankin.
Wannan sako na iske gwamnatin Kaduna sai ta fantsama aiki, ta kai kukan ta ga rundunar soji dake aikin samar da tsaro a jihar Bauchi, Filato da yankunan Kaduna, wato rundunar ‘Operation Safe Haven.
Cikin gaggawa sai dakarun wannan runduna suka dira wannan daji da motocin yaki.
Sojoji sun karade wannan daji da tsauni tun daga kasa har sama amma basu ga ko da alama ce ta wasu sun taba ma zama a wannan tsauni ballantana wai har su yada zango su maida wani yanki na tsauni maboyar su don aikata ta’addanci a kudancin Kaduna.
Sojojin sun karade tsaunin da da wannan daji kaf, babu wani abu mai kama da haka.
Kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro na kasar har Kaduna, Samuel Aruwan ya jinjina wa dakarun sojin bisa namijin kokari da suka yi na garzaya wannan daji kai tsaye bayan samun rahotan.
A karshe ya hori mutane su da su rika sabar da jami’an tsaro bayanan sirri game da ayyukan ‘yan ta’adda sannan kuma maimakon a rika daukan fansa idan abu ya faru a gaggauta kai sanar da hukuma.
Lambobin sanar da gwamnati bayanai kai tsaye:09034000060, 08170189999