Mataimakin Gwamnan Jihar Ondo, Agboola Ajayi, wanda ya fice daga jam’iyyar APC ya koma PDP, ya bayyana cewa babu wani dalilin da zai sa ya saka daga matsayin sa na Mataimakin Gwamna Rotimi Akeredolu saboda ya fita daga APC.
Ya shaida wa wakilin mu, ta bakin kakakin sa Tope Okeowo cewa, “tare aka zabi Gwamna Akeredolu da Ajayi. Kuma shi Ajayi din ya na da kishin yi wa al’umma aiki.
“Sannan dokar Najeriya ta ba da iznin kowa zai iya shiga jam’iyyar da ran sa ya fi so. Doka ta tabbatar da haka lokacin Obasanjo, tsakanin sa da Atiku Abubakar, Mataimakin sa a lokacin.
“Kuma ba wannan ne karo na farko da mataimakin gwamma ko wani gwamna ya fice daga wata jam’iyya.
Mataimakin dai ya je mazabar sa ta 2_ Apoi, cikin Karamar Hukumar Ese-Odo, ya yi rajista da jam’iyyar PDP.
Ajayi ya samu sabani da Gwamna Akeredolu, bayan ya nuna sha’awar sa ta tsayawa takarar gwamna tare da Akeredolu.
Cikin dare a ranar Asabar, an yi rincimi tsakanin mataimakin gwamnan da Kwamishinan ‘yan Sandan Ondo, Bolaji Salami, wanda ya hana shi fita gidan gwamnati da motar gwamnati wadda ake a hannn sa.
Ajayi dai ya ce shi ya Sayi motar da kudin sa. Shi kuma Gwamna Akeredolu ya ce ba shi ya ingiza kwamishinan ‘yan sanda ya hana mataimakin sa Ajayi fita da motar ba.