2018 ZUWA 2020: Kwatagwangwar rikicin APC 10 da Buhari ya kasa sasantawa cikin shekaru biyu

0

Wadannan kadan ne daga manyan rikice-rikicen da suka afka wa jam’iyyar APC, ko kuma wadanda APC din ta rufta a cikin su a shekaru biyu kacal. Abin lura a nan, ana magana ne a kan wadanda su ka fi yi wa jam’iyyar mummunar illa.

Jam’iyyar APC ta kafa mulki a cikin 2015 tare da gwamnoni 22, APC 11, APGA 1. Amma tun mulkin na ta bai cika shekaru biyar ba, akala da linzamin takun siyasa sun subuce, ta yadda rigingimun hadama da ‘ninanci’ da kuma sakaci su ka haifar ma ta asarar kujerin gwamnoni.

Ya zuwa yanzu, APC na da gwamnoni 17, PDP 16, sai APGA 1.

Ga wasu manyan rigingimun da suka dabaibaye APC cikin shekaru biyu, wadanda Buhari ya kasa sasantawa, kuma su ka taru suka haifar wa jam’iyyar gagarimar asara.

1. Buhari ya kasa sasanta Minista Rotimi Amaechi da Sanata Magnus Ibe. Hakan a karshe ya sa APC ta yi asarar kujerar gwamna, sanatoci uku, dukkan wakilan Majalisar Tarayya da na jihar Ribas.

2. Buhari ya kasa sasanta tsohon gwamna Abdul’aziz Yari da Sanata Marafa, hakan ya janyo wa APC asarar kujerar gwamna, sanatoci, Mambobin Majalisar Tarayya da na jihohi a Zamfara.

3. Kasa sasanta Gwamna Ganduje da Sarki Muhammadu Sanusi (murabus), wanda Ganduje ya zarga da mara wa PDP baya. Wannan ya janyo karsashin Buhari ya ragu a kasar nan bayan cire Sarki Sanusi. Kuma kwarjinin sa ya yi kasa a Kano, a lokacin da Ganduje ya yi “aikin Gama ya Gama domin neman cin zabe ido-rufe.

5. Kasa sasanta Mataimakin Gwamnan Kogi da Gwamna Yahaya Bello. A karshe sai da aka tsige mataimakin. Masu nazarin siyasa na ganin cewa karsashin Buhari ya yi nakasu ganin yadda Gwamna Bello ya yi amfani da kamfen din ‘ratatatata tatatatata’ kafin ya ce zabe.

5. Kasa sasanta tsohon gwamnan Lagos, Akinwumi Ambode da Bola Tinubu kafin zaben 2019. Jama’a na ganin cewa Tinibu ke dorawa ya sauke gwamna, ba al’umma ba a karkashin mulkin Buhari.

6. Kasa sasanta Gwamnan Godwin Obaseki da Adams Oshiomhole, wanda a yanzu haka sakamakon sa APC ta rasa jihar Edo, tunda Gwamna ya koma PDP daga APC.

8. Kasa sasanta Gwamnan Kaduna Nasiru El-Rufai da Sanata Shehu Sani.

Share.

game da Author