A ranar Alhamis ne BudgiT ta fitar da wannan bayani cike da al’ajabin yadda ake facaka da kudade karkashin wannan gwamnati, inda ake bayyanan yadda ake kashe kudade a hanyoyi da tsarin da ke cike da mishkila.
Dalla-Dalla a nan:
1. BudgiT ta shiga cikin rumbum, ta rungumo takardun bayanai 600 na yadda aka yi biyan kudade sau 100,000.
2. BudgiT ta gano cewa tsakanin watan Janairu zuwa Yuli, 2019, an biya makudan bilyoyin kudade a cikin aljifan wasu mutane, maimakon kamfanoni.
3. BudgiT ta gano daruruwan bayanan biyan makudan kudade wadanda duk baddalallu ne, babu takamaimen ainihin adireshi ko sunan kamfanin da aka biya kudin.
4. An kafci makudan bilyoyin kudade an biya daidaikun mutanen da ga sunayen su nan baro-baro (maimakon a ce sunayen kamfanoni ne aka biya kudaden a cikin asusun su na banki).
5. An biya sama da mutum 2,000 naira bilyan 51, naira bilyan 2.04 da kuma wasu naira bilyan 1 a cikin watan Yuni, 2019.
6. Misalin irin wannan biyan kudade, shi ne, an biya wani mai suna Ogunbiyi naira milyan 68. (Babu sunan kamfanin sa ballantana aikin da ya yi aka biya shi kudin).
7. An biya naira milyan 15.8 ga wani suna wai shi “International” kawai. Babu wani cikakken bayani banda kalmar ‘International.’
8. Cikin 2019 an biya kudade kashi-kashi har sau 5,000 ga sunayen da babu wani cikakken bayani da zai iya gano ko su wane ne ko wadanne kamfanoni ne aka biya kudaden.
Adadin kudaden da aka biya a cikin wannan shekara a wannan bayani mai daure kai, sun kai naira bilyan 278.
9. An biya wata jimillar naira bilyan 275 a kididdigar biyan kudade 4360 daban-daban, amma duk babu ko da sunan wanda aka biya kudin. (Sai dai a rubuta an biya naira kaza kawai).