Kwamitin dakile yaduwar cutar Covid-19 na jihar Sokoto ya bayyana cewa an sallami duk wadanda suka kamu da Covid-19 sannan aka killace sua wuraren da aka kebe don killace masu dauke da cutara a jihar.
Shugaban kwamitin Ali Inname ya sanar da haka da yake hira da manema labarai a garin Sokoto ranar Juma’a.
Inname ya ce kada wannan nasara da jihar ta samu ya sa jama’a su shafa’a su yi sakwa-sakwa da bin dokokin hukumar NCDC sa saka na yadda za a kiyaye da kauce wa duk hanyar da zai sa a kamu da cutar.
Inname ya yi kira ga mutane da su rika zuwa asibiti a duk lokacin da ba su da lafiya yan mai cewa gwamnati ta inganta asibitocin jihar da wadata su da magunguna domin mutanen jihar.
Ya yi kira ga mutane da su ci gaba da kiyaye sharadun gujewa kamuwa sa cutar domin dakile yaduwar cutar a jihar.
Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 328 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Juma’a.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Juma’a, sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum 131, FCT – 70, Bauchi – 25, Rivers – 18, Oyo – 16, Kaduna – 15, Gombe – 14, Edo – 12, Ogun – 13, Jigawa – 8, Enugu – 6, Kano – 5, Osun – 2, and Ondo – 2
Yanzu mutum 11,844 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 3696 sun warke, 333 sun mutu.
Duk da yawan mutane da ake samu sun kamu da cutar a kullum a Najeriya, wasu da dama na ganin har yanzu ba a yi wa mutane gwajin cutar yadda ya kamata a kasar.
Jihar Legas na ci gaba da samun daruruwan mutanen da suka kamu da cutar Korona babu kakkautawa.
A ranar Juma’a kawai, jihar Legas ta samu karin mutum sama da 130.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 5, 663 cases, followed by Kano – 985, FCT – 862, Katsina – 385, Edo – 364, Oyo – 334, Kaduna – 335, Borno – 322, Ogun – 329, Jigawa – 282, Rivers – 308, Bauchi – 281, Gombe – 184, Sokoto – 115, Kwara – 127, Plateau – 113, Delta – 116, Nasarawa – 90, Zamfara – 76, Ebonyi – 80, Yobe – 52, Osun 49, Akwa Ibom – 45, Adamawa – 42, Niger – 41, Imo – 47, Kebbi – 33, Ondo – 38, Ekiti – 25, Enugu – 30, Bayelsa – 30 Taraba – 18, Abia–15, Benue – 13, Anambra – 12, and Kogi – 3.