WATA SABUWA: Yadda aka cika runbum ajiyar bayanan kashe kudaden Gwamnatin Najeriya makil da algusshu – BudgiT

0

Kungiyar BudgiT, mai sa ido kan yadda hukumomin gwamnati ke kashe kudade, ta tabbatar da cewa rumbun ajiyar kididdigar bayanan yadda ake kashe kudaden gwamnati (portal), ya na yoyon da mai yiwuwa da gangan aka huda shi.

BudgiT ta ce rumbun cike makil da daburtaccen lissafi, bayanai masu dungu, karkatattun lissafe-lussafe da kuma yadda aka yi wuji-wuji da bilyoyin nairori aka damka su ga wadansu daidaikun mutanen da dokar kwangila ta haramta aiwatarwa da aikata haka.

A ranar Alhamis ne BudgiT ta fitar da wannan bayani cike da al’ajabin yadda hakan ke faruwa a karkashin wannan gwamnati, inda ake bayyanan yadda ake kashe kudade a hanyoyi da tsarin da ke cike da mishkila.

Daya daga cikin wadanda suka kirkiro BudgiT, mai suna Seun Onigbinde ne ya fitar da wadannan hardaddun bayanan da ya ce kungiyar su ta leka ta gano a cikin rumbun ajiyar bayanan kididdigiar.

Bayan yin wannan bayani, sai kuma Babbar Jami’ar Sadarwar BudgiT, mai suna Damilola Ogundipe, ta fitar da takarda mai dauke da kididdigar fallasar da kungiyar ta bankado.

BudgiT ta ce gwamnatin Buhari ta yi zurfin tunanin kirkiro rumbun ajiyar cikin Disamba, 2019 domin tattara bayanan yadda kowace Ma’aikata, Hukuma da Cibiyoyin Gwamnatin Tarayya ke kashe kudaden gwamnati ga ayyukan da ta ke yi.

“Wannan tsari ne mai kyau, amma kuma abin mamaki cike ya ke da algusshu, bankaura da bayanan lissafe-lissafen harambe, wadanda dokar kashe kudade ta haramta irin su.

“Saboda haka akwai bukatar yi wa rumbun garambawul a cikin gaggawa, domin ya nuna jama’a za su rika zargin irin yadda gwamnati ke kashe kudade ta hanyoyin da ba bisa ka’ida ba.” Inji BudgiT.

Abin Mamaki A Karkashin Gwamnatin Buhari:

1. BudgiT ta shiga cikin rumbum, ta rungumo takardun bayanai 600 na yadda aka yi biyan kudade sau 100,000.

2. BudgiT ta gano cewa tsakanin watan Janairu zuwa Yuli, 2010, an biya makudan bilyoyin kudade a cikin aljifan wasu mutane, maimakon kamfanoni.

3. BudgiT ta gano daruruwan bayanan biyan makudan kudade wadanda duk baddalallu ne, babu takamaimen ainihin adireshi ko sunan kamfanin da aka biya kudin.

4. An kafci makudan bilyoyin kudade an biya daidaikun mutanen da ga sunayen su nan baro-baro (maimakon a ce sunayen kamfanoni ne aka biya kudaden a cikin asusun su na banki).

5. An biya sama da mutum 2,000 naira bilyan 51, naira bilyan 2.04 da kuma wasu naira bilyan 1 a cikin watan Yuni, 2019.

6. Misalin irin wannan biyan kudade, shi ne, an biya wani mai suna Ogunbiyi naira milyan 68. (Babu sunan kamfanin sa ballantana aikin da ya yi aka biya shi kudin).

7. An biya naira milyan 15.8 ga wani suna wai shi “International” kawai. Babu wani cikakken bayani banda kalmar ‘International.’

8. Cikin 2019 an biya kudade kashi-kashi har sau 5,000 ga sunayen da babu wani cikakken bayani da zai iya gano ko su wane ne ko wadanne kamfanoni ne aka biya kudaden.

Adadin kudaden da aka biya a cikin wannan shekara a wannan bayani mai daure kai, sun kai naira bilyan 278.

9. An biya wata jimillar naira bilyan 275 a kididdigar biyan kudade 4360 daban-daban, amma duk babu ko da sunan wanda aka biya kudin.
(Sai dai a rubuta an biya naira kaza kawai).

Share.

game da Author