Domin tabbatar da ganin an samu amfani mai yawa a noman bana gwamnatin tarayya ta Babban bankin Najeriya, CBN za ta agaza wa manoman dake tsarin shirin gwamnati na ‘Anchor Borrowers Programme (ABP)’ akalla su miliyan 1.6.
Jami’in CBN Yila Yusuf ya Sanar da haka ranar Talata a taron raba wa manoman auduga a garin Kwali a Abuja.
” Gwamnati za ta tallafawa manoman auduga 256,000 ta tsarin shirin ta na ABP domin karfafa gwiwowin manoman auduga a kasar nan.
“Manoma za su karbi tallafin ne a matsayin bashi bayan sun yi girbi amfanin gona za su biya bashin da riba.
“A dalilin annoban coronavirus gwamnati ta rage ribar da manoman dake karkashin shirin ABP Za su biya daga kashi 9 zuwa 5 bisa 100.
A watan Nuwamban 2015 ne gwamnati Muhammadu Buhari ta kirkiro shirin ‘Anchor Borrowers Programme (ABP)’ domin inganta aiyukkan noma a kasar nan da tallafa wa manoma.
Manoman dake karkashin shirin ABP na samun tallafin kayan aikin noma a matsayin bashi wanda za su biya da zarar sun yi girbi.
A farkon shirin ABP gwamnati ta raba wa kananan manoman da suka yi rajista da shirin Naira biliyan 220 a kasar nan.
Da yawa daga cikin wadanda suka karbi bashin kudin basu iya biyan wannan basussuka da suka karba ba da hakan yasa a bana a ka rage ribar.
Discussion about this post