Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya sassauta dokar hana bude wuraren kasuwanci da sauran wuraren mua’muloli a jihar.
El-Rufai ya amince musulmai su rika sallar Juma’a sannan Kiristoci su rika fita zuwa ibada a coci ranar Lahadi.
Baya ga haka ba a amince a rika yin salloli biyar da aka saba ba, kuma makarantu da manyan kasuwannin jihar duk za su ci gaba da zama a garkame sai bayan an sake yibwa dokar garambawul.
Bayan haka matafiya daga kananan hukumomin jihar Kaduna za su iya ci gaba da shiga da fice daga garuruwa.
Duk wuraren kasuwanci da zasu bude, su tabbata sun samar da na’urar gwajin yanayin zafin jikin mutum, ruwan wanke hannaye, da man tsaftace su.
Haka kuma suma Otel a fadin jihar duk za su iya budewa domin ci gaba da ayyuka, saidai kuma dole su kiyaye dokokin da aka saka ne.
Suma ma’aikatan gwamnati za su dawo aiki kamar yadda shugaban ma’aikatan jihar za ta sanar nan gaba.
Sannan kuma gwamnati ta ce a hankali za ta ci gaba da tattaunawa da shugabannin kasuwanni da makarantu domin tsara yadda za a bude su ba tare da an samu matsala ba.
Mutum 363 suka kamu da kwayoyin cutar Korona a jihar Kaduna. Anyi wa mutum 2485 gwajin cutar. An sallami mutum 210, mutum 11 sun rasu.
Discussion about this post