Yawan shan magani a lokacin da mace ke al’ada na hana haihuwa – Likita

0

Kwararriyar likita akan dawainiyar haihuwa na mata, Abosede Lewu ta yi kira ga mata da su rage yawan shan magani dake rage laulayi a lokacin al’ada a cewa yin haka na lalata mahaifar mace.

Lewis wacce Jami’ar Kungiyar ‘Keep All Mothers Alive (KAMA)’ ce ta ce yawan shan magani musamman ga budurwa wacce bata haihuwa ba a lokacin da take haila na iya hana haihuwa.

” Mafi yawan mata kan yi amfani da wasu kwayoyi a lokacin da suke al’ada domin rage radadin al’ada amma kuma hakan babban hadari ga mace domin yakan illata mahaifarta ta kagara haihua a gaba.

Lewu ta yi kira ga mata da su daina shan ire-iren wadannan magunguna domin kada ya illata su.

Hanyoyin rage laulayi da radadin al’ada ga mata

1. Motsa jiki; Ba sai mace ta tashi tana tsalle-tsalle ba ko kuma guje-guje ba mace za ta iya motsa jiki a cikin gidan ta ta hanyar aiyukkan cikin gida

2. Amfani da ruwan zafi; Da zaran mace ta fara al’ada ta rika wanka da ruwan dumi, sannnan ta rika shan shayi mai zafi.

3. Hutu kamar barci na rage ciwon kai da zazzabin da akan ji a lokacin haila.

4. Dabarun bada tazaran hihuwa; Wasu likitoci sun ce amfani da dabarun bada tazaran haihuwa zai taimaka wajen rage laulayin haila.

5. Cin wasu kayan abinci dake kara wa mutum karfin garkuwa; A lokacin da mace ta fara al’ada kamata ya yi ta rika cin kayan bincike dake dauke da sinadarin inganta garkuwan jiki.

Share.

game da Author