Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, karkashin Mai Shari’a Taiwo Taiwo, ta kara jaddada wa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), karfin ikon soke rajistar duk wata jam”iyyar da ta Kasa cika sharuddan zama jam’iyya bayan gudanar da zaben Shugaban Kasa.
A ranar Juma’a ce kotu ta yanke hukunci cewa INEC ta yi daidai da ta soke rajistar Hope Democratic Party (HDP) da sauran jam’iyyun da ta soke, saboda sun kasa cika sharuddan da kundin mulki sashe na 225(a) ya samar.
HDP ce ta Kai kara ta nemi a hana INEC soke ta da ma sauran wasu jam’iyyu da ta soke.
INEC ta soke jam’ iyyu 74 cikin 91 ta bar 18 kacal, bisa dalilin cewa sun kasa yin nasara a ko da zabe daya da hukumar ta gudanar a shekarar 2020.
Cikin watan Mayu ma INEC ta yi nasara a kan jam’iyyar National Unity Party (NUP), saboda an soke ta ita ma.
Soke jam’iyyun barkatai da INEC ta yi ya zo daidai lokacin da jama’a da dama ke korafin cewa yawan jam’iyyun barkatai ba shi da wani muhimmanci, sai ma kara harfar da kashe kudade wajen gudanar da zabe.
Wata babbar matsala kuma da jam’iyyu barkatai suka haifar a lokacin zabe, ita ce yadda masu jefa kuri’a da dama suka rika rudewa su kasa gane jam’iyyar da suka yi niyyar jefa wa kuri’a, saboda yawan jam’iyyun.