Daga cikin nadin mukaman siyasa 190 da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi bayan sake zaben sa a 2019, Jihar Ogun ce ta fi sauran kowace jihar kasar nan samun mukamai masu yawa.
Cikakkun bayanan da PREMIUM TIMES ta samu daga Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, sun nuna cewa Ogun ta samu mukamai 17, sai ta biyu da ta uku Adamawa da Jihar Kano kowacen su na da mukamai 14.
Jihar Lagos da Oyo kowacen su na da rabon mukamai 12. Jihohin Katsina, Osun, Edo da Ondo kowace Buhari ya nada mukamai 8.
Buhari ya nada mukaman siyasa ga mutane 7 daga jihar Katsina da Kwara.
Yayin da ya nada mutum 6 daga jihar Delta, mutum 2 daga Yankin Babban Birnin Tarayya, Abuja (FCT), Buhari ya nada mutum 1 tal daga kowace jiha, a cikin Bayelsa, Ebonyi, Imo, Filato, da kuma Zamfara.
Idan aka auna rabon mukaman a bisa sikeli na shiyya, Shiyyar Kudu maso Yamma (Lagos, Ogun, Oshun, Ogun, Ondo da kuma Ekiri) ce ta fi samun mukamai har 64.
Arewa maso Gabas inda Buhari ya fito (sun samu mukamai 37. Su ne jihohin Katsina, Kano, Kaduna, Jigawa, Zamfara, Sokoto da Kebbi.
Shiyyar Arewa maso Gabas kuwa mai jihohin Yobe, Adamawa, Barno, Taraba, Bauchi da Gombe su na da mukamai 29.
Shiyyar Kudu maso Kudu mai jihohin Akwa Ibom, Bayelsa, Rivers, Cross River, Delta da Edo, na da mukamai 24.
Arewa Ta Tsakiya (Neja, Benuwai, Nassarawa, Filato, Kogi da Kwara na da mukamai 21.
Shiyyar Kudu maso Gabas mai Anambra, Abia, Enugu, Ebonyi da Imo sun samu mukamai 15.