KORONA: Dalilin da ya sa gwamnati jihar Legas ta janye bude wuraren Ibada a jihar

0

A ranar Talata ne gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya sanar cewa gwamnati ba za ta bude bude wuraren ibada ba, wato masallatai da coci a jihar.

A baya dai gwamnati ta ce zata amince wa wuraren ibada su bude daga ranar Talata.

Sanwo -Olu ya ce gwamnati ta canja wannan shawara ne ganin yadda annobar Korona ke ci gaba da yaduwa a jihar kamar wutar daji.

” Har yanzu fa jihar Legas ne ke kan gaba wajen samun yawan mutanen dake kamuwa da cutar. Hakan ya sa dole mu ci gaba da yin kaffa-kaffa da kula matuka kafin mu amince wuraren ibada su bude.

Sanwo-Olu ya ce sakamakon gwajin cutar da Hukumar NCDC ta fitar ranar Litini ya nuna cewa akalla mutum sama da 7,300 sun kamu da cutar a jihar Legas.

Daga ciki an sallami mutum 1,137, mutum 82 sun mutu sannan 6,100 na kwance suna jinya.

Gwamnan ya yi kira ga mutanen jihar da su ci gaba da kiyaye sharuddan kauce wa kamuwa da cutar.

A karshe Sanwo-Olu ya ce jihar zata ci gaba da wayar wa mutane kai kan yadda za su kiyaye kan su da kuma mahimmancin yin gwajin cutar. Sannan kuma ya hori mutane da su kiyaye dokokin da aka saka don kauce wa kamuwa da cutar.

Abuja ce take bi wa jihar Legas a yawan wadanda suka kamu da cutar sai kuma jihar Kano.

Share.

game da Author