Dalilin shirya Zanga-zangar lumana a Katsina – Kungiya

0

Daruruwan mutane sun amsa kiran kungiyar da ta shirya yi wa Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari zanga-zanga ta lumana a Katsina, a ranar Talata.

Masu zanga-zangar dai sun fara tattaki ne dauke da kwalaye, daga Fadar Mai Martaba Sarkin Katsina Abdulmumin Kabir har zuwa Tsohon Gidan Gwamnatin Jihar Katsina.

Kungiyar ‘Coalition of Northern Youth ce ta shirya zanga-zanga da hadin guiwar wata kungiyar ta kasa baki daya.

An shirya zanga-zangar ce domin nuna rashin jin dadin yadda Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi sakacin kyale ‘yan bindiga na ta kashe mutane babu kakkautawa a jihar Katsina da ma sauran jihohin Arewacin Najeriya.

Shugaban shirya zanga-zangar Tanimu Charanci, ya ce ya zama tilas su fito su nuna rashin jin dadin yadda aka yi sakacin barin ‘yan bindiga suke kashe mutane a jihohi daban-daban na Arewacin kasar nan.

Shi kuwa Shugaban na Kasa bakidaya. Nastura Sheriff, ya ce za a yi irin wannan zanga-zanga ta lumana a ranar Asabar mai zuwa a jihohin Arewa gaba daya.

Ya kuma yi kira ga Buhari ya cire manyan hafsoshin tsaron kasar nan. Ya ce a yanzu dai su da Gwamnatin Buhari da ta dora su, duk sun gaza.

“Mun gaji da kullum wayewar gari sai dai Shugaban Kasa ya fitar da takardar yin tir da kashe-kashen da ake yi, amma ya kasa kawo karshen wannan kashe-kashe.”

“Mun Yi Sak, Mun Kasa Sakewa, Mun Kasa Mun Tsare, An Kasa Tsare Mu. Mun Raka, An Bar Mahara Sun Rarake Mu” -Masu Zanga-zanga

Wadannan kalamai da ke sama na daga cikin wasu kalaman da ke rubuce a kan wasu kwalaye da masu zanga-zanga suka rike a Katsina.

Cikin watan Janairu 2012, Buhari ya ja zugar tattaki a Abuja, inda su ka yi wa Gwamnatin Goodluck Jonathan tattakin nuna damuwa kan karin kudin litar man fetur da kuma matsalar tsaro, har Buhari ya nemi Jonathan ya sauka idan ba zai iya kare ‘yan Najeriya ba.

Share.

game da Author