‘Yan sanda sun cafke Dagace da Faston da suke yi wa yara kanana Fyade

0

Rundunar ‘yan sannan jihar Akwa-Ibom ta damke wani Fasto da dagacen kauyen Ikot Inyang da ake zargin su da laifin yi wa rara kanan fyade

Kakakin rundunar ‘Yan sandan N-nudam Fredric ya sahida cewa dagacen kauyen Ikot Inyang dake karamar Hukumar Ibesikpo-Asutan, Okon Uyoe ya yi lalata da wata yarinya mai tallan kosai da karfin tsiya bayan ya lallabata ta bi shi ciki.

” Bayan dagacen ya cinye kosan da wannan ‘yar talla take saida wa sai ya lallabe ta suka ta fi dakin sa domin ya bata kudin kosan, daga nan ne fa ya danne ta da karfin tsiya yayi lalata da ita.

Fredric ya kara da cewa an tabbatar da wannan basarake ya aikata wannan mummunar aiki ne ranar 13 ga watan Yuni da misalin karfe 1:12 na rana.

Haka kuma yan sandan sun cafke wan fasto mai suna Victor David da aka samu shima ya yi lalata da wata yar sa shekara 8.

Fredric ya ce David ya danne wannan yarinya ne bayan iyayen yarinyar sun aiko ‘yar su da sakon madaran gwan-gwani a kawo wa faston.

A karshe dai Fredric ya ce dukkan su za su fuskanci hukunci.

Idan ba a manta ba Sufeto Janar na Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya bayyana cewa an samu rahotannin fyade har sau 717 tsakanin watan Janairu zuwa karshen Mayu.

Share.

game da Author