Shugaba Muhammadu Buhari ya janye dokar Zaman Gida Dole da ya saka a jihar Kano na makonni biyu.
Sakataren gwamnatin Tarayya, kuma shugaban kwamitin shugaban Kasa Kan dakile yaduwar annobar Korona, Boss Mustapha ya shaida cewa Shugaba Buhari ya janye dokar hana walwala da ya saka a jihar Kano makonni biyu da suka gabata.
Mustapha ya ce gwamnati za ta bayyana sabbin tsare-tsare domin ci gaba da Kare mutane daga Korona.
Sai dai kuma ko da Shugaba Buhari ya saka wannan doka, gwamnatin Kano karkashin gwamna Abdullahi Ganduje, warware wannan doka, in da ta amincewa wa mutanen jihar su halarci Sallar Idi da Juma’ar makon da aka yi idin karamar Sallah.
Jihar Kano na da sama da mutum 900 da suka kamu da cutar cikin mutum sama da mutum 10,000 da suka kamu a Najeriya.
Haka kuma Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya janye dokar dakatar da Sallah a masallatai da zuwa coci da gwamnati ta saka domin dakile yaduwar Korona a kasar nan.
” Daga ranar 2 ga watan Juni za a fara zuwa masallaci yin salloli da kuma coci domin yin bauta kamar yadda aka Saba a da. Za a ci gaba da haka daga 2 ga wata zuwa 29 ga watan Juni.
Buhari ya ce bayan wadannan makonni hudu da aka saki mutane su rika halartar masallatai da coci, gwamnati zata sake duba yadda mutane suka yi biyayya ga umarni da dokokin gwamnati domin sake yi wa umarnin garambawul.
Discussion about this post