Buhari ya janye dokar dakatar da Sallah da zuwa Coci

0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya janye dokar dakatar da Sallah a masallatai da zuwa coci da gwamnati ta saka domin dakile yaduwar Korona a kasar nan.

Hakan ya biyo bayan shawarwarin da kwamitin shugaban kasa kan dakile yaduwar annobar Korona ya ba Shugaba Buhari da kuma matakan da gwamnoni suka dauka don tabbatar da kauce wa yaduwar cutar jihohi.

” Daga ranar 2 ga watan Juni za a fara zuwa masallaci yin salloli da kuma coci domin yin bauta kamar yadda aka Saba a da. Za a ci gaba da haka daga 2 ga wata zuwa 29 ga watan Juni.

Buhari ya ce bayan wadannan makonni hudu da aka saki mutane su rika halartar masallatai da coci, gwamnati zata sake duba yadda mutane suka yi biyayya ga umarni da dokokin gwamnati domin sake yi wa umarnin garambawul.

Share.

game da Author