Gwamna Bello ya Garkame karamar hukuma saboda zargin bullar Korona

0

Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya sanar da saka dokar Zaman Gida Dole na makonni biyu a karamar Hukumar Kabba-Bunu, dake jihar.

Gwamna Bello ya ce ya yi haka ne domin gudanar da bincike mai zurfi game da zargin da aka yi wai limamin Kabba, ya rasu a dalilin kamuwa da Korona ne da yayi.

Gwamna Bello ya ce ba su amince da haka ba da ya sa dole jihar zata gudanar da nata sahihin binciken da gwaji domin gano ainihin abinda yayi sanadiyyar rasuwar limamin, Abubakar Ejibunu.

” Tun bayan bayyana cewa jihar Kogi ta samu mutum biyu, da suka kamu da cutar a jihar, muka gaggauta kwashe makusantan marigayin su 13 domin ayi musu gwajin jin cutar. Dukkan su basu da ita kamar yadda Sakamakon gwajin ya nuna.

” Bayan haka a gaskiya hukumar NCDC bata kyauta Mana ba, da ta lallabo da Yi abinda ta ga dama, ta koma ta ce wai an samu mutum biyu da suka kamu da cutar a jihar. Ba ta sanar da gwamnatin jihar ba kawai ta yi gaban kanta.

” Mu dai a jihar Kogi bamu da Korona ko da daya ne, wadanda ake rubutawa wai an samu ba haka bane. Ana so dole da karfin tsiya sai mun ce muna da wanda ya kamu da cutar. Ba zamu yi haka ba.”

A karshe gwamna Bello ya ce jihar na ci gaba da yin kira ga mutane su bi dokokin hukumar NCDC na Kare Kai daga kamuwa da cutar.

Share.

game da Author