BINCIKEN KWAKWAF: Yadda Gwamnatin Buhari ta shafe shekaru hudu ta na tattake dokar sharuddan korar sojoji daga aiki

0

Ga duk mai so ya san yadda Gwamnatin Najeriya ta kwance zanin wanda ya yi mata bauta, ta bar shi tsirara a tsakiyar kasuwa, to ya karanta sakayyar da aka yi wa Kanar Mohammed Sulaiman, wanda saboda tsananin sadaukar da kan sa da ran sa da ya yi wajen yaki da ta’addanci a kasar nan, har lambar girmamawa aka ba shi a cikin 2012.

To kuma ga duk mai son jin irin sakayyar da aka yi wa Sulaiman da wasu hafsoshin sojojin 37, a cikin 2016, kamata ya yi ya ma fara jin irin jarumta da sadaukarwar da wannan hazikin soja ya yi wa Najeriya tukunna.

1. Shi ne ya hargitsa mummunan tuggun shirin Boko Haram na kai wa Fadar Shugaban Kasa hari a 2012. An tsara yunkurin tare da hannun wani dan sanda mai suna Babagana.

PREMIUM TIMES ta tabbatar da haka a cikin wani kwafen takardun bayanai na mahukuntan soja.

2. An sha tura Sulaimam aiki a Darfur a Kudancin Sudan da Washington a Amurka, amma sai a fasa tura shi, saboda muhimmancin aikin da ya ke yi na tsaro a kasar nan.

3. Ya na tsakiyar aikin bayar da horo a Kwalejin Sojoji ta Jaji, aka kira shi a gaggauce, ya tsara yadda aka kama wani gawurtaccen dan Boko Haram na farko, mai suna Adam Kambar, wanda duniya da Amurka aka rika nema ruwa-jallo.

4. Sulaiman ne ya shirya yadda aka kama gawurtaccen kwamandan Boko Haram, Umar Sanda Kadunga, Wanda Kuma shi ne kakakin Boko Haram.

5. Shi ne ya kirkiro tunanin kafa jami’an tsaro na hadin-guiwa, wato CJTF a Barno.

6. Sulaiman ne ya fara tattara bayanan sirri dangane da ayyukan Boko Haram, tun kafin ma kungiyar ta fara yin karfin da ta fara Kai hare-hare a Jihar Bauchi.

7. Cikin 2009 ya shirya kai wa Boko Haram mummunan farmakin da aka yo nasarar kama 377, aka kashe wasu, ba tare da an yi asarar soja ko daya ba.

Yadda Aka Yi Masu Ritayar Dole

To wannan jarimin Kanar na soja ne aka wayi shi da wasu manyan sojojin Najeriya 37, suka wayi gari safiyar 9 Ga Yuni, 2016 kowa ya ga an turo masa takardar sallama daga aikin soja, a shafin sa na e-mel, a bisa yi masu ritayar-dole.

“To ni dai abin nan ya ba ni mamaki da al’ajabi. Ba ta taba Kama ni da laifi ba. Ba a taba ba ni takardar gargadi ku gurfanar da ni an tuhume ni a kan wani laifi ba.” Inji Laftanar Kanar Abdulfatah Mohammed.

Bayanan sallamar ta su daga aiki ba wani mai tsawo ba ne. Yanko wata aya aka yi daga cikin Kudin Dokar Aikin Soja a Shashin Ladabtarwa da Kira Aiki. Sai aka rubuta cewa: “An ladabtar da su ne, saboda sun aikata gagarimin laifi.

Amma fa ba a ce ga laifin da kowanen su ya aikata ba.

Haka dai aka bayanna cewa an yi amfani da wannan Sashi na 09.02c (4) an hukunta su.

Sai dai kuma waahegari a ranar 10 Ga Yuni, sai Kakakin Sojoji na Lokacin, Burgediya-Janar Mai Ritaya a yanzu, Sani Usman, ya bayyana cewa an sallame su ne saboda sun yi katsalandan cikin sha’anin zaben 2015.

BINCIKEN da PREMIUM TIMES ta yi ya gano cewa yawancin sojojin ba a tuhume su ba ballantana a same su day laifi. Wasu kuma an tuhume su, ba a same su day laifi ba, amma kuma an yo musu ritayar-dole. Kalilan ne aka samu da laifi daga cikin wadanda aka sallama din.

Yadda Gwamnatin Buhari Ke Take Umarnin Kotun Da Ta Ce A Maida Sojojin Aikin Su:

Shekaru hudu kenan ana tabka shari’a a Kotun Ma’aikata (Industrial Court), inda Sulaiman da wasu sojoji biyar suka you nasara, kotu ta bada umarnin a maida su bakin aikin su.

Sau 6 kenan kotu na bada umarnin a maida sojoji, amma sau shida Gwamnatin Tarayya na sa kafa ta na tattake wannan umarnin kotu.

Sau shida ‘Industrial Court’ na ayyana cewa an cire sojojin ta haramtacciyar hanya. Don haka a maida su bakin aikin su.

Wannan tattake umarnin kotu na daya daga cikin yadda ake yi wa gearzaye kuma zaratan da suka bauta wa kasar su bahaguwar sakayya a kasar nan.

Daya daga cikin wadanda aka sallama din mai suna Ochankpa Ojebo, ya mutu a cikin 2017, ya na cike da haushi da kuncin bakin-cikin irin sallamar da aka yi masa daga aikin soja.

Buhari Ya Yi Biris Da Rokon Da Su Sulaiman Suka Yi Masa:

A karkashin dokar da a ka yi amfani da ita aka sallame su, akwai inda aka yarda za su iya aikawa da takardar rokon maida su aiki ga Shugaban Kasa.

Ana rubuta wannan wasika ce cikin kwanaki 30 daga ranar da aka sallame su. PREMIUM TIMES ta tabbatar da cewa sun rubuta wasikar, amma shekara hudu kenan har yau ba su ji komai ba daga Fadar Shugaban Kasa.

ManjoJanar-Janar Din Da Aka Jefa Cikin Tasku:

Akwai wasu Manjo Janar wadanda sun gurfana a gaban Kwamitin Bincike, ba a same su da laifi ba, amma kuma an yi masu ritayar-dole. Sun hada da:

1. S.D Aliyu (N/7711)
2. M.Y Aliyu (N/8114)
3. Fatai Ali (N/7914)

Manjo Janar 5 da aka sallama ba tare da tuhuma ko samun su da laifi ba:

Su wadannan sun ce ba wanda ya gayyace su zuwa Kwamitin Bincike, ballantana a tuhume su har a same su da laifi, kamar yadda Dokar Kira Daga Aikin Soja ta tanadar. Amma duk da haka aka sallame su.

1. L. Wiwa (7665). Kanin Ken Saro Wiwa ne.
2. Nwokwo Ije (8304). Cikin 2019 kotu ta ce a maida shi aiki
3. T.C Ude (7866)
4. L.C Ilo (8320)
5. O Ejemau (8340)

Jangwangwama Da Jekala-jekala:

Majiya ta tabbatar cewa an sallami wasu Burgediya Janar su 11, saboda zargin sun ki taimaka wa wannan gwamnatin a zaben 2015.

Akwai ma Kanar-kanar da Laftanar-Kanar da yawa da aka yi wa ritaya bisa zargin sun taimaka wa PDP a zaben 2015.

Kamar dai wasu Kanar bakwai da PREMIUM TIMES ta binciko cewa an yi musu ritaya ba tare da tuhuma, bincike ko samun su da laifi ba. Cikin su har da Kanar Mohammed Sulaiman.

Majiya ta ce an yi wa O.C Egemkle, Kwamandan Bataliya ta 93 da ke Takum ritaya, saboda ya bari APC ta kasa yin nasara a Jihar Taraba, a zaben 2015.

Share.

game da Author