BARNO: Gwamna Zulum ya sake damka gidaje 100 ga wasu masu gudun hijira daban a Bama

0

Gwamna Babagana Zulum na jihar Barno ya bayyana kwace wasu sabbin gidaje 100 da aka raba wa ‘yan gudun hijira, ya sake damka su ga wasu masu gudun hijira a Bama.

Ciikin shekarar 2019 ne hamshakin attajiri Mohammed Indimi ya gina rukunin gidaje 100 ya damka wa gwamnati a Bama domin ta raba wa masu gudun hijira.

Bayan an raba gidajen, daga baya gwamnatin jihar ta gano cewa duk ba a zauna cikin gidajen ba.

A wata ziyarar da Zulum ya kai Bama, ya bada umarnin soke hakkin mallakar zaman gudajen ga wadanda aka damka wa shekarar da ta gabata.

Da ya ke jawabi a Fadar Sarkin Bama, Umar Ibn Kyari El-Kanemi, Zulum ya ce:

“Daga yau na soke damka gidajen ga wadanda aka damka wa su da farko. Bai yiwuwa a damka wa mutum gidan zama a Bama, alhali shi kuma ya na Maiduguri a zaune.

“Ina kira ga Mai Martaba Sarki da ya gaggauta tattara sunayen mutanen kauyen Yaudari da ke gudun hijira, ya damka musu gidajen kawai.

Zulum ya kuma raba kayan abinci ga masu gudun hijira su 25,000, wadanda ya ce kayan abincin na hadin-guiwa ne daga gwamnatin tarayya da ta jihar Barno.

Zulum ya kuma jaddada cewa nan ba da dadewa ba za a kwaso mutanen kauyukan Nguro Soye, Banki da Gulumba a maida su gidajen su, daga garuruwan Menawo da Kirana, inda yanzu haka su ke gudun hijira a cikin kasar Kamaru.

Da ya juya a Bama kuwa, Zulum cewa ya yi abin takaici ne shekaru biyar kenan yaran Bama ba su zuwa makaranta.

A kan haka ya ce gwamnatin sa ta shirya nan ba da dadewa ba, da guguwar Coronavirus ta wuce, za a bude makarantu, tare da daukar sabbin daliban sakandare da na firamare.

Share.

game da Author