Babban Bankin Tarayya, CBN ya bayyana cewa ya ware zunzurutun kudi naira bilyan 432 domin tallafawa inganta noman wasu amfanin gona guda 9, a daminar 2020.
Amfanin gonar da za a ware kudin domin noman su, sun hada da noman shinkafa, kiwon dabbobi, noman rogo, masara, auduga, man ja, kiwon kaji da kuma noman kifi.
CBN ya ce wannan shiri aka yi domin inganta Tsarin Lamunin Bunkasa Manoma (Anchor Borrowers’ Programme), yadda abinci ba zai yanke a wannan shekara ba.
Hukumar Kididdigar Alkaluman Bayanai ta Kasa (NBS), Tsadar rayuwa a watan Mayu Najeriya ta yi kuncin da ba ta yi ba tsawon watanni 25 baya.
Hukumar Kididdigar Alkaluman Bayanai ta Kasa (NBS), ta bayyana cewa an samu tsadar rayuwa a Najeriya a cikin watan Mayu, fiye da watanni 25 da suka wuce a baya.
NBS ta ce tsadar rayuwa ya karu da kashi 12.4 a cikin watan Mayu da ya gabata.
Hukumar Kididdigar wadda mallakin gwamnatin tarayya ce, ta ce tashin gwauron zabin da kayan masarufi ce ta haddasa wannan hauhawar kuncin rayuwar.
Sai dai kuma ta jingina manyan sabubban kuncin rayuwar a kan barkewar cutar Coronavirus daga watan Maris a kasar nan da ma duniya baki daya.
Rahoton Kididdigar Hawa Da Saukar Farashin Kayan Masarufi (Consumer Price Index) da aka fitar a ranar Laraba, ya nuna yadda farashin kayayyakin ya haura daga 12.34 a watan Afrilu zuwa 12.4 a cikin watan Mayu da ya gabata.
Kididdigar tsakanin watan Mayu na shekarar da ta gaabta zuwa Mayu na watan jiya, ya nuna farashin hauhawa kawai ya rika yi, bai rika raguwa ba, ballantana ya rika yin faduwar-‘yan-bori, daga 11.71 zuwa 11.79 a watan jiya.
Farashin kayan abinci ya fi tashi a Abuja, Osun da Imo. Amma na jihohin Abia, Bauchi da Kaduna bai yi muni kamar na su Abuja din ba.
A Ebonyi da Bayelsa da Zamfara ma farashin kayan abinci irin tashin cilkowa sama ya yi.
Rahoton ya nuna jihar Akwa Ibom ce kadai aka samu rangwamen farashin kayan abinci da na masarufi.
Tallafin Noma Na CBN:
Babban Bankin Najeriya ya ce ya zama wajibi a bayar da wannan lamuni ga kananan manoma da masu kananan masana’antu, domin ceto su daga radadin kuncin da Coronavirus ta jefa milyoyin jama’a.
Daraktan Bunkasa Hada-hadar Kudade, Yila Yusuf ya ce CBN zai bayar da kudaden ta hannun wasu bankuna.
Ya ce sama da manoma milyan 1.1 ne wadanda za su noma sama da hekta milyan daya za a raba wa ramcen kudaden.
Yusuf ya ce ana sa ran za su noma akalla metrik tan milyan 8.3 na kayan abinci.
Makasudin wannan lamuni dai shi ne a tabbatar cewa manoma sun koma gona, duk kuwa da cewa Coronavirus ta sa da dama daga cikin su sun ji jiki a wannan shekara.
Wakilan Kungiyoyin Manoma da suka hakarci taron sun yaba wa CBN. Daga cikin wadanda suka halarta, akwai RIFAN, NACOTAN, Kungiyar Masu Noman Masara, Kungiyar Masu Casar Masara, MAGPMAN da sauran su.