Hukumar Kuka Da Masu Gudun Hijira Ta Majalisar Dinkin Duniya, ta bayyana cewa akwai kusan masu gudun hijira milyan 2.4 a yankin Arewa maso Gabas na Najeriya.
Hukumar ta ce wadannan masu gudun hijira duk rikice-rikicen yakin Boko Haram ne ya haddasa su, wanda ya fi kazamcewa a Yankin Tafkin Chadi.
Kwamishinar Hukumar UNHCR, Chansa Kwoaya ce ta bayyana haka a wurin taron tunawa da zagayowar Ranar ‘Yan Gudun Hijira ta Duniya, Abuja.
Kapaya ta ce a cikin Jihohin Barno, Adamawa da kuma Yobe akwai masu gudun hijira milyan 1.8.
Ta ce akwai dimbin masu gudun hijira a yankin Sahel, cikin Nijar, Kamaru da Chadi.
Da ta ke karin bayani, Kapaya ta ce akwai masu gudun hijira su 57,000 daga Kamaru wadanda ke zaune a Najeriya.
Wasu masu gudun hijira da ta yi magana kuma su ne adadin 2,340 da ke zaune a birane. Inji ta akwai wasu 1,122 da ke neman mafaka a Lagos, Ogun, Kano da kuma Abuja.
“Sannan akwai kuma ‘yan Najeriya su 292, 141 masu gudun hijira a Nijar, Kamaru da Chadi.
UNHCR ta ce ta na bakin kokarin ta wajen hana Coronavirus barkewa a sansanonin masu gudun hijira.
Sannnan kuma ta kafa cibiyoyin bincike da na killacewa, a daidai kan iyakokin kasar nan.